Da dumi-dumi - JIRGIN FARKO NA MAHAJJATAN KATSINA YA BARO JEDDA

Da dumi-dumi - JIRGIN FARKO NA MAHAJJATAN KATSINA YA BARO JEDDA
 
Sama da awa guda da ta wuce, jirgin farko dauke da mahajjatan jahar ya baro Jedda da karfe 2 da minti 48 agogon Najeriya zuwa Katsina. Mahajjatan sama da 400 sun fito daga shiyyar Daura. Yanzu haka dai suna bisa iska acikin jirgin Max Air 5N-HMM (NGL 2022 VM 2022) wanda ke cikin sararin samaniyar Egypt a yayin wannan rubutu. A sa ran wajen karfe 8 zuwa 9 da daren wannan rana ta laraba cikin ikon Allah zasu sabka a filin jirgin Umaru Musa 'Yar'aduwa dake cikin garin Katsina. 

Post a Comment

Previous Post Next Post