Da dumi dumi - JIRAGEN MAX AIR ZASU DAWO AIKI DAGA 30 GA WATAN YULI, 2023

Da dumi dumi - JIRAGEN MAX AIR ZASU DAWO AIKI DAGA 30 GA WATAN YULI, 2023

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Jiragen sama na kamfanin Max Air da aka bayar da sanarwar dakatar da su daga zirga-zirga cikin gida a kwanan nan saboda wasu dalilan da aka ambata wanda a ciki har da batun yin amfani da gurɓattan mai, a yanzu jiragen zasu ci gaba da zirga-zirgar su kamar yadda aka saba.
Wata sanarwar da ta fito daga mahukuntan kamfanin ta tabbatarwa da masu hulda da jirage da sauran jama'a cewar, jiragen zasu ci gaba da hidimomin nasu daga ranar Lahadi 30 ga watan Yuli 2023 in Allah ya kaimu. Akan haka suka yi kira ga jama'a musamman masu mu'amulla da kamfanin na Max Air a ciki da wajen Æ™asa cewar, kamfanin a shirye yake na ganin ya kyautatawa abokan huldar shi. Kazalika, kamfanin na Max Air yayi kira ga jama'a da su guji yaÉ—a labaran da basu da tabbaci akan shi musamman akan abin da ya shafi harkokin jiragen na Max Air 

Post a Comment

Previous Post Next Post