BAYAN SABKAR JIRGIN ALHAZAI NA 7 NA 8 NA NAN TAFE GOBE
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A yayin da ake cigaba da maido mahajjatan da suka aiwatar da aikin Hajjin 2023 a gidajen su a fadin duniya baki daya, Jahar Katsina na daya daga cikin jihohin Najeriya da mahajjata sama da dubu 4 suka sabke wannan farali daga cikin ta ke kokarin kwaso nata mahajjatan zuwa Kazalika, kamar sauran hukumomin jin dadin alhazai na duniya nan ma jahar na daga cikin sahun na gaba-gaba da suke bakin iyakar yin su na ganin sun kyautatawa alhazan su.
Har'ila yau, gurin kowane mahajjaci ne yaga ya dawo gida acikin lokaci bayan kammala wancan aiki na farilla. Bisa wannan yunkurin ne duk da 'yan tsaikon da ake samu, Jahar ta Katsina a ranar larabar nan 26 ga watan Yuli hukumar tayi nasarar kawo mahajjata 546 tare da ma'aikata 10 a jirgi na 7 ta hanyar jirgin Max Air 5N-HMM Boeing 747-4B5 VM2026 mallakin hamshakin dan kasuwar nan Alhaji Dahiru Mangal a babban filin sabka da tashi na jiragen sama na Umaru Musa Yar'adua dake cikin birnin Katsina.
Mafi yawan mahajjatan da aka zanta da su dangane da korafin da suka rika yi na samun tsaikon kwaso su, sunce rashin fahimta ko sanin yadda lamarin kwasowar ne yasa suka fara korafin, amma daga baya da suka fahimci haka, sai ma su mayar da hankalin su a wajen zuwa yin ibada a can Harami.
Da muka tuntubi Babban Daraktan hukumar Jin dadin alhazan Alhaji Sulemain Nuhu Kuki akan cewa, ana ganin shi a filin na Sarki Abdul Aziz dake Jedda tare da masu ruwa da tsaki akan aikin, ko suna da nufin dawowa gida ne duk da aikin bai ƙare ba? Sai ya amsa da cewar, sun yanke shawarar biyo mahajjatan ne har zuwa Jedda domin gani tare da tabbatar da cewa, an dauke su cikin lokacin da aka aiyana ba tare da samun wata matsala, kazalika, ganin nasu tare da alhazan yana karawa alhazan kwarin guiwar cewa sun tabbata hukuma bata yi watsi da su ba kamar yadda ake yi a wasu wuraren. "Duk lokacin da muka tura alhazan mu domin yin dawafin bankwana, to muna nan tare da su tun daga dauko daga Makka har zuwa Jedda tare kuma da ganin tashin jirgin su don zuwa gida. Tun daga jirgin farko, har zuwa wannan na 7 bamu samu wata matsala ba. Alhazai da su kan su masu jiragen muna samun fahimtar juna sai dai azijanci kawai wanda kuma ba za'a ce an rasa samu ba.
Kamar yadda ASKGLOC NEWS suka samu labari, jirgi na 8 na mahajjatan Jahar ana sa ran zowar su gida a ranar Alhamis 27 watan Yuli 2023