ƊANMAJALISAR TARAYYA YA BA MAHAJJATAN MUSAWA DA MATAZU TALLAFIN RIYAL 100

DANMAJALISAR TARAYYA YA BA MAHAJJATAN MUSAWA DA MATAZU TALLAFIN RIYAL 100
Hon. Abdullahi A. Ahmed Talban Musawa 

Ɗanmajalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Musawa da Matazu Honarabil Abdullahi Aliyu Ahmed Talban Musawa ya baiwa kowane mahajjacin da ya fito daga ƙananan hukumomin Musawa da Matazu tallafin Riyal 100 na kuɗin Saudiyya waɗanda suke kwatankwacin naira dubu ashirin kowane mutun.
Da yake hannantawa mahajjatan kudin a madadin Ɗanmajalisar, Sarkin Musawan Katsina Alhaji Sagir Abdullahi Inde wanda kuma shi ne Daraktan sashen kudi na hukumar jin dadin alhazan ya ce, wannan tallafi na daga cikin irin aiyukan alherin da shi Talban Musawan ke aiwatarwa ga al'ummar shi, don haka ya ja hankalin mahajjatan da su yi amfani da kudin ta hanyar da ta dace ganin cewa yanzu an kammala aiyukan ibadar ta bana. Akwai bukatar mahajjatan su yi taka tsantsan wajen sayan guzuri duba da cewa, akwai sauran 'yan kwanaki kafin su koma gida. Don haka su kara mayar da hankali wajen ganin sun yi abin da ba zai cutar da su ba, musamman sayen kayan da zasu sa a wajen awo a fitar da su saboda sun wuce nauyin da ake bukata. 
Ɗanmajalisar ya nemi mahajjatan da su cigaba yiwa ƙananan hukumomin su, jiha da kasa addu'o'in samun zaman lafiya da karuwar arziki acikin sauran kwanakin da suka rage masu, musamman a lokacin da suka je yin dawafin neman wata biyan bukatar su. 
Da yake bayanin godiya a madadin sauran mahajjatan da suka karbi wannan tallafi wanda yace ba lallai sai ya ambaci sunan shi ba, sai dai yana magana da sunan mutanen su baki daya, ya jinjina tare da yiwa wannan Ɗanmajalisar tare da hakiman su musamman shi Sarkin na Musawa da ya dauko wannan nauyi na amana Allah kuma ya bashi ikon sabkewa. "A madadin mahajjatan da muka fito daga ƙananan hukumomin Musawa da Matazu muna yiwa Talban Musawa addu'ar Allah yasa yadda ya hau mulkin shi na wakiltar mu a matakin kasa lafiya, Allah yasa ya gama lafiya. Allah yasa wata rana muce mun tafi Katsina wajen Gwamna (dariya da tabi). Shi ma Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda muna yi mashi addu'ar fatan sabke nauyin da Allah ya aza ma shi lafiya, shi ma wata rana mu ce, zamu Villa wajen Shugaban kasa. Kuma in sha Allahu zamu ci gaba da yiwa kananan hukumomin mu da jahar mu da kasa baki daya addu'o'in neman zaman lafiya da karuwar arziki. Mun gode. 

Post a Comment

Previous Post Next Post