ALHAZAN SHIYYAR KATSINA KANKIYA DA HEDKWATA SUKA RAGE A YANZU

ALHAZAN SHIYYAR KATSINA KANKIYA DA HEDKWATA SUKA RAGE A YANZU
Da misalin karfe 10 da minti 45 jirgin mahajjatan na biyar na jahar Katsina su 414 da suka fito daga shiyyoyin Daura, Mani, Malumfashi da Funtuwa sai wasu daga Dutsinma suka sabka a filin Jirgi na Umaru Musa 'Yar'adua dake garin Katsina.
Kamar yadda jami'in hulda da jama'a na hukumar jin dadin alhazan na Jahar Katsina Alhaji Badaru Bello Karofi ya shaida, a yanzu sauran alhazan shiyyar Katsina da Kankiya da kuma ita Hedkwata suka rage wadanda su ma ake cigaba da shirye-shiryen kwaso su bayan kammala aikin hajjin na 2023.
Jirgin wanda yake mallakin kamfanin Max Air ne mai lamba 5N-BBN VM5014 ya baro Jedda da misalin karfe 5 da minti 42 agogon Najeriya, ya kuma sabka lafiya da misalin karfe 10 da minti 45 cif. 

Post a Comment

Previous Post Next Post