JIRGI NA 5 YA DAUKI MANIYATAN JAHAR KATSINA 315 ZUWA MADINA

JIRGI NA 5 YA DAUKI MANIYATAN JAHAR KATSINA 315 ZUWA MADINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

Da misalin karfe É—aya da rabi na dare jirgi na biyar ya tashi zuwa Madina bayan ya É—an yada zango a Abuja domin cikawa da maniyatan Lokoja daga Jahar Kogi. Jirgin Max Air mai lamba NGL 3017 ADM ya dauki maniyatan jahar ta Katsina su 315,maza 185,mata 130. Ana sa ran zai kwashi sauran ragowar maniyata 230 daga Abuja, wata na Jahar ta Kogi.
Maniyatan da jirgin na Max Air ya dauka sun fito daga shiyyar Dutsinma, wato ita kanta Dutsinmar, Batsari, Danmusa, Safana da kurfi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post