GWAMNA RADDA YA KAI ZIYARA ASIBITI A KATSINA

GWAMNA RADDA YA KAI ZIYARA ASIBITI A KATSINA  
Daga  Kabir Ahmed S/Kuka
 Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda ya kai wata ziyarar ba zata a asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya dake nan cikin garin Katsina. Gwamnan ya kai wannan ziyarar dubiya ta ba zata da safiyar yau Asabar. Gwamna Radda ya zagaya dakuna daban daban na marassa lafiya. A wannan ziyarar dubiya Gwamna Malam Umar Radda ya biyawa wasu majiyata 35 kudaden magunguna duba da irin halin da suke ciki. Gwamna Radda ya yaba da irin halin da yaga asibitin take ciki wajen kula da marasa lafiya. Ziyarar Gwamnan ta samu tarba daga shi Shugaban wannan asibiti Dokta Suleiman Bello Muhammad

Post a Comment

Previous Post Next Post