Da dumi-dumi - JIRGI NA SHIDDA YA TASHI DAGA KATSINA - MADINA

Da dumi-dumi - JIRGI NA SHIDDA YA TASHI DAGA KATSINA - MADINA
Daga Kabir Ahmed S/kuka

(Hoto na nuna taswirar da jirgin ya bi don zuwa kasar ta Saudiya, bayan awa É—aya da wasu 'yan mintuna da tashin shi) 
Da misalin karfe 12:05am(na dare) Jirgin Max Air ya tashi daga filin sabka da tashi na jirgin sama wato, Umaru Musa International Airport dake cikin garin Katsina dauke da maniyata 541 cikin su har da ma'aikata 2. Jirgin mai lamba NGL 3029 Boeing 747-4B5 5N HMM ya tashi da maniyatan da suka fito daga shiyyoyin Daura, Mani, Dutsinma, Malunfashi da Funtua don kai su Madina a bisa hanyar su ta sabke farali. Maza 209 da mata 232. Su dai wadannan maniyata sun samu tsaikon tashi har na kwana biyu sanadiyyar wata matsala da aka samu daga jirgin da zai kwashe su zuwa kasar ta Saudiya kamar yadda Amirul Hajjin Honarabil Musa Tasi'u Maigari ya shaidawa wakilin ASKGLOC NEWS 'yan mintuna bayan tashin jirgin. Sai dai Amirul Hajjin ya tabbatarwa sauran maniyatan da suka rage cewar da ikon Allah za'a cigaba da daukar su ba tare da wani jinkiri ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post