DA dumi dumi - JIRGI NA BIYU DAGA KATSINA YA TASHI ZUWA SAUDIYA

DA dumi dumi - JIRGI NA BIYU DAGA KATSINA YA TASHI ZUWA SAUDIYA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Yanzu cikin daren nan jirgin Max Air ya dauki maniyatan da suka fito daga Æ™ananan hukumomin Dutsi, Mani, Mashi, Kafur da kuma Kankara suka tashi zuwa Æ™asar Saudiya domin yin aikin Hajjin 2023. 
Su dai wadannan maniyata da suka haurawa 500 sun baiyana jin dadin su na ganin zasu tashi domin zuwa wannan aiki na ibada bayan sun kwana da yini a filin tashi da sabka na jiragen sama na Umaru Musa 'Yar'aduwa dake cikin garin Katsina sakamakon wata 'yar matsala da wanj jirgin na kamfanin Max Air da ya samu yayin da ya dauko maniyatan Jahar Jigawa inda jirgin yayi sabkar gaugawa a Kano domin samun dauki daga injiyoyi don komawa cikin hayyacin shi. Waccan matsala ce tasa dole kamfanin ya bayar da jirgin da zai dauki maniyatan na jahar Katsina wanda yake zaman jiran su, yayin da a hannu guda anan Katsina ana cikin tantance maniyatan da zai dauka. 
Kamar yadda wani maniyacin da ya nemi a sakaya sunan shi yace, "da farko rai na ya baci ganin irin yadda na zaunu anan ba tare da sanin makoma ta ba, amma a yanzu sai naji dadi ganin cewa jirgi ya sabka don ya kwashe mu zuwa can Saudiya. Akan haka ne ma na yafewa duk wani wanda yasa raina ya baci. Kuma wannan hakuri da muka yi ni da abokina(cikin murmushi) ya kara tabbatat mana da cewa, lallai aikin Hajji hakuri da juriya su suka fi yawa a wajen gudanar da shi". 
Ita ma wadda tace sunan ta Nana, tace da farko har ta fidda rai, amma yanzu sai taji wani sabon karfi ya zo mata. Su kan su jagororin hukumar jin dadin alhazan da masu ruwa da tsaki ga gudanar da aiyukan sun ta kaiwa da komowa na ba maniyatan hakuri gami da ci gaba da yi masu wa'azi na tunasarwa akan yadda aikin yake tafiya. Dokta Aminu Yamma da Hajiya Binta 
Mai Larabci na a sahun gaba na wajen ba maniyatan hakuri tare da yin wa'azin. 

Post a Comment

Previous Post Next Post