AN SANYAWA TASHAR KOFAR 'YANƊAKA SUNAN GWAMNA RADDA

AN SANYAWA TASHAR KOFAR 'YANƊAKA KATSINA SUNAN GWAMNA RADDA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Alhaji Dalha Halliru shugaban ƙungiyar 

Ƙungiyar direbobi NURTW reshen Tashar Ƙofar' Yanɗaka ta sanyawa tashar sunan Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda. Sanyawa tashar Gwamnan ya biyo bayan rushe sayar da filayen gwamnati ba bisa ƙa'ida da tsohuwar gwamnatin Masari ta yi wanda cikin waccan sayarwa har da tasoshin mota guda 5 da suka haɗa da Tashar Kofar Durbi, Kofar Marusa, Kofar Sauri, Kofar Guga da kuma ita Kofar 'Yandaka. Sayar da waɗannan tasoshi ya tayar da hankali matafiya ganin irin nisa da kuma ƙarin kuɗin ababen hawa.
Damuwar sayar da tasoshin bai tsaya akan fasinjojin ba kawai, hatta da ƙungiyar direbobi na waɗannan tasoshi sun nuna damuwar su akan irin yadda wannan lamari zai gurguntar da sana'ar ta su da kuma irin yadda wasu wuraren da aka yi ƙoƙarin mayar da tasoshin zasu shiga cikin haɗarin matsalar tsaro musamman ita tashar ta Kofar 'Yandaka. 
Da yake shaidawa wakilin ASKGLOC NEWS Shugaban ƙungiyar NURTW dake Kofar 'Yandaka Alhaji Dalha Halliru ya ce, sun yanke shawarar sanyawa tashar sunan daga tashar Kofar 'Yandaka zuwa "Tashar Malam Dikko" domin nuna farin cikin su akan yadda ya ceto rayuwar su daga shiga garari, wanda matsalar tuni ta shafi wasu mutanen dake cin abin ci acikin ta.
    Allon sunan da aka sanyawa tashar sunan Gwamnan Malam Umar Radda 

"Tuni har wasu sun faɗa cikin halin rashin lafiya yayin da wasu jarin nasu ya fara shiga cikin hali saboda zullumi da rashin sanin halin da ake ciki. Mutun yana zaune cikin shago kawai sai Dillali ya zo yace in kana son shagon to ka fara neman fansar shi domin an sayarwa wani. Sannan wanda aka amshewa babu wata diyya ko tallafi, kawai an amshe".
Shugaban ƙungiyar a dogon bayanin da ya yiwa wakilinmu a ofishin sa dake cikin tashar ya ƙara da cewa, jin waccan sanarwa ta soke sayar da filayen da shi Gwamna Radda yayi, sun ji dadin ta wanda yasa har taron gaugawa suka yi domin yiwa Gwamnan addu'o'i na musamman bayan karata Al-Ƙur'ani mai Girma. Sannan ya ƙara da cewa, tun daga wannan rana sun yanke shawarar bashi goyon baya don ganin ya samu nasara a mulkin shi wanda suke fatan yayi wa'adi biyu kafin ya wuce ga kujerar shugaban ƙasa. 
Wasu daga cikin masu harkokin su na neman abinci shekara da shekaru sun nuna farin cikin su akan wannan mataki da Gwamnan ya ɗauka. Malam Abubakar Usman tsohon shugaban ƙungiyar da Malam Lawal Abu Mataimakin Shugaban ƙungiyar da kuma Malam Aminu Abba mai tsawatawa acikin ƙungiyar na daga cikin mutanen da suka tofa albarkacin bakin su akan wancan yunƙuri da kuma sanyawa tashar sunan Gwamnan. Masu maganar sun yiwa Gwamnan fatan alheri da kuma addu'ar Allah ya cigaba da yi mashi jagora ga wannan jagorancin al'umma da yake yi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post