ALHAZAN JAHAR KATSINA NA SAMUN ABINCI CIKIN LOKACI

ALHAZAN JAHAR KATSINA NA SAMUN ABINCI CIKIN LOKACI

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
A yayin da alhazai ke cikin shirin dawo daga zaman Mina don Æ™arasa jifar Shedan a Jamret a gobe juma'a. Alhazan Jahar Katsina na ci gaba da samun abinci akan kari bayan fuskantar 'yar matsalar da aka samu ta karancin masabkai acan garin na Mina duk kuwa da zafin ranar da aka samu. Lamarin da yashi jihohi da dama na Najeriya da ma wasu Æ™asashen. 
A wannan zama na Mina har zuwa ranar da mahajjata zasu dawo garin Makka, hukumar kula da aikin Hajji ta Æ™asa NAHCON ita ke da alhakin samar da masabkai da kuma abinci ga maniyatan har zuwa ranar dawowa garin Makka inda lamarin ya koma hannun hukumomin jin dadin alhazai na jihohi. A iya cewa, jahar Katsina ta fuskanci irin wannan matsala, amma kuma sai jami'an hukumar karkashin jagorancin Babban Daraktan hukumar Alhaji Sulemain Nuhu Kuki suka yi gaugawar daukar mataki don ganin cewa maniyatan da suke jagoranta basu shiga cikin garari ba. 
Wani mahajjaci mai suna Alhaji Bishir da muka tuntuba acan garin na Mina ya shaida mana cewar, farko gaban shi ya fadi kuma ya fara shiga cikin wani tunanin rashin tudun dafawa, ganin cewa, bai samu inda zai aza kafadun shi balle ya nemi abinci. Sannan a ranar farko irin yadda yaga anyi wasoso wanda har wasu mata basu samu ba. "Gaskiya ganin wannan ya tayar mani da hankali ganin wannan shine zuwa na farko. Amma a yanzu kam, sai godiya ga Allah, domin har naje wajen jifa a yau na dawo na taras da an ajiye mani nawa abincin. Sai ince hukumar jin dadin Alhazai tayi rawar gani, domin naga har yanzu wasu makwabtan mu basu shawo kan matsalar ba". 
Da aka tuntube shi akan wannan lamari da kuma irin hanyar da suka biyo suka shawo kan wannan matsala, Babban Daraktan hukumar Alhaji Sulemain Nuhu Kuki yace, "duk da cewa alhakin wurin kwana da ciyarwa yana hannun NAHCON hakan ba zai sanya mu rike hannuwan ba musamman idan muka lura da cewa akwai wata matsala. Wannan ne yasa muka yi taron gaugawa na masu ruwa da tsaki da suka hada da shi Amirul Hajj da Shugaban kwamitin aikin da sauran ofishin mu don samun hanya mafita ga alhazan. Anan ne muka yanke shawarar kiran jagororin alhazai na kananan hukumomi da ake kira "Desk Officers" muka mika masu alhakin karbarwa mutanen abincin in an kawo. Munyi haka ne saboda ganin cewa, su ne suka san mutanen su. Hakan kuma zai kawo mana karshen masu shigar burtu acikin mutanen, wato, tukari, dake amfani da wannan dama. A hslin su bamu da wata matsala ta batun abinci hatta da wajen kwanan domin Allah cikin ikon shi yasa munyi nasara akan wannan dabara da muka bullo da ita".
Babban Daraktan yace, in baya ga rasa wani mutun guda daga shiyyar Funtuwa wanda Allah ya karbi rayuwarsa babu wata matsalar azo a gani da ake fuskanta

Post a Comment

Previous Post Next Post