ZA'A YI TARON WAYAR DA KAI GA MANOMAN ALKAMA AKAN SANIN DABARUN NOMAN ZAMANI A JAHAR KATSINA
Qungiyar manoman Alkama ta qasa reshen Jahar Katsina ta shirya haɗa hannu da wasu hukumonin ayyukan gona domin bunƙasa noman Alkama ka'in da na'in a Jahar a wannan damana. A labarin da muka samu hukumomin da ƙungiyar zata yi aikin tare da su sun haɗa da Bankin bunƙasa ƙasashen Afirka (African Development Bank) da babban Banking Nigeria CBN da wata ƙungiyar larabawa dake ƙasar Dubai. Shugaban qungiyar noman alkama na jahar Katsina Alhaji Hassan Salihu ƙwai ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi. Alhaji Hassan Salihu ƙwai ya ce, "maƙasudin yin hakan shi ne domin a tallafawa manoman Alkamar na jahar da dabarun noma irin na zamani da bayar da basussuka da nagartattun iri, da samar da taki da sauran tallafi domin bunƙasa noman allkamar.
Shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa, tuni ƙungiyar ta kammala dukkanin shirye shiryen da suka dace domin kankamar wannan shirin a jahar ta Katsina. Yace "za a gudanar da wani taron fadakarwa ga manoman Alkamar a shiyyoyi uku na jahar da suka haɗa da Daura da Katsina da kuma shiyyar Funtuwa domin ilmantar da su akan shirin. Alhaji Hassan Salihu ya nuna damuwarsa akan yadda mafiyawan 'yan ƙungiyar da suka amfana da bashin Babban bankin Najeriya CBN na "Anchor Borrower" da na "Private Anchor" tun a shekarar 2018 ya zuwa yau basu biya ba". Anan sai yayi kira ga irin waɗannan manoman dasu biya waɗannan basussuka domin kaucewa ɗaukar mataki akan su.
Shugaban kungiyar ya bayyana cewa duk wanda bai biya wannan bashi ba to ba zai amfana da wannan shiri da ake ƙoƙarin gudanarwa domin bunƙasa manoman alkamar ba. Alhaji Hassan yace domin cin nasarar fara gudanar da shirin ƙungiyar ta samar da wasu takardu domin masu bukatar shiga shirin su cika. A ƙarshe Shugaban ƙungiyar ya godewa Babban Bankin Nigeria CBN da Gwamnatin Tarayya da ta jahar katsina akan tallafi da goyon baya da suke baiwa sha'anin noman alkama a jahar katsina.