Hajj 2023 - KADA A ƘARAWA MANIYATA KUDI

Hajji 2023 - KADA A ƘARAWA MANIYATA KUDI - Cibiya
Anyi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su dubi halin da ake ciki, kada su ƙarawa maniyatan aikin Hajjin wannan shekara kudin jirgi wanda sanadiyar fadan da ake yi a kasar Sudan wanda ya janyo ragayen hanya da jiragen sama zasu yi kafin isa kasar Saudiya ta dalilin rufe sararin samaniyar kasar ta Sudan wadda ta nan ne maniyyatan daga Najeriya suke bi. 
Wata cibiya mai zaman kanta dake kawo rahotannin aiyukan Hajji da Umra daga ciki da wajen kasa wadda ake kira "Independent Hajji Reporters" tayi wannan kira bayan samun wani rahoton da ta samu daga hukumar dake kula da aiyukan Hajji ta kasa, NAHCON akan batun karin kudin jirgin. A rokon da cibiyar ta yi dangane da wannan batu ta ce, " a ranar Asabar Hukumar dake kula da aiyukan Hajji ta Ƙasa NAHCON ta bayar da sanarwar biyan ƙarin dalar Amurka 250 na kuɗin Hajjin biyo bayan kulle sararin samaniyar ƙasar Sudan sakamakon yaƙin da ƙasar ke fama da shi".
"Kuɗin kujerar Hajjin da aka ƙayyade ga maniyyatan Nijeriya da farko, ya shafi keta sararim samaniyar Sudan ɗin ne zuwa Saudiyya, wanda akan yi hakan ta la’akari da sa’o’in da jirgi zai shafe kafin ya isa Saudiyya daga Sudan. Bayan biyan kuɗin aikin Hajji da aka amince, mun san cewa Musulmin Nijeriya ko maniyyatan Nijeriya za su biya bambancin kuɗin titkitin jirgi idan lokaci ya ba da dama.
Cibiyar ta ci gaba da cewa,ta damu akan wannan batu ne wanda ya ta so a lokacin da ya rage ƙasa da kwanaki 10 a fara jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa kasar ta Saudiyya don sabke wannan farali. Saboda haka, buƙatar maniyyata su sake biyan wani kuɗi a daidai wannan lokaci zai haifar da cikas wajen aikin jigilar maniyyatan. 
 Wannan roko dai ya fito ne a wata sanarwar da babban mai kula da cibiyar (CSO) na ƙasa, Ibrahim Muhammad, ya fitar a ƙarshen mako. “Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihohi da su haɗa kai da Hukumar Hajji ta Nijeriya  (NAHCON) sannan su ɗauke wa maniyyatan jihohinsu ƙarin kuɗin da aka buƙaci a biya sakamakon sararin samaniyar Sudan zai kasance a rufe kafin fara jigilar maniyyata. Har ila yau, Muna roƙon Gwamnatin Tarayya ta ɗauki kashi 50 cikin 100 sannan jihohi su biya ragowar kashi 50 ga maniyyatan da suka fito daga yankunansu domin basu damar zuwa wannan aiki mai muhimmamci ga musulmi. 
Indai za'a tuna, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince jiragen Saudiyya da wasu daga Nijeriya da suka haɗa da Max Air, Air Peace, Azman Air, Aero Contractors, Arik Air da kuma Value Jet su yi aikin jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasa mai tsarki. An zaɓi jirage biyar na farko a kan su yi jigilar maniyyata daga jihohi 36 har da Abuja, su kuwa jiragen Arik da Value Jet an ɗora musu aikin jigilar maniyyatan da za su tafi Hajjin a zaman kansu, wadanda ake yiwa lakabi da jirgin yawo. 
Bisa ga wannan hali da ake ciki, jirgin Saudiyya ne kaɗai ya amince a kan zai yi jigilar maniyyatan Nijeriya a kan farashin da aka ƙayyade tun farko, inda ake sa ran ya yi jigilar maniyyata 28, 515. 
Sauran jiragen cikin gida da suka buƙaci a yi musu ƙarin su ne: Max Air wanda zai kwashi maniyyata dubu 16,326 sai Air Peace wanda zai kwashi maniyata dubu 11,348, Azman Air zai ɗebi maniyata dubu 8,660 sannan Aero Contractors ya tashi da maniyyata 7,833, yayin da za a bar ragowar jimillar maniyyata 44,167 daga jihohi daban-daban cikin halin rashin tabbas.
Rufe sararin samaniyar Sudan ta tilastawa jirage yin tafiya mai nisan zango kafin isa Saudiyya, wanda za a shafe aƙalla sa'o'i 7 ana keta hazo maimakon awa 4 da ɗoriya da aka saba. Wannan matsalar ta haifar da ƙarin sa'o'i 2 zuwa 3 a farashin jigilar maniyyatan da aka cimma tun farko na jimlar kudi kusan naira milyan uku wanda tuni maniyatan suka kammala biyan acikin wa'adin da aka ba su na 21 ga watan Afrilun da ya wuce kamar yadda NAHCON ta sanar can baya. 
Cibiyar ta ƙara da cewa, “Yayin da muke yaba ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya wajen nasarar kwashe 'yan Nijeriyan da suka maƙale a Sudan, a hannu guda muna kira ga gwamnatin da ta sake maimaita irin wannan abin yabon ta hanyar saussautawa maniyyatan Nijeriyan kuɗin jirgi don samar da damar aiwatar da aikin Hajjin na cikin natsuwa 2023", kamar yadda shugaban Cibiyar Ibrahim Muhammad yayi rokon. 

Post a Comment

Previous Post Next Post