Hajj 2023 - AN FARA TARON BITAR MANIYATAN JAHAR KATSINA DA ƘAFAR DAMA

Hajj 2023 - AN FARA TARON BITAR MANIYATAN JAHAR KATSINA DA ƘAFAR DAMA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
Dangane da shirye-shiryen da take yi akan aikin Hajjin 2023 wanda ake sa ran farawa acikin wannan wata na Mayu, hukumar Jin dadin Alhazai ta jahar Katsina karkashin shugabancin Babban Daraktan hukumar Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ta fara yin taron bita ga maniyatan da zasu sabke farali a wannan shekara domin basu damar sanin yadda aikin Hajjin yake don su yi aikin karbabbe.
Taron bitar wanda aka fara a karshen makon da ya gabata bisa kulawar shugaban sashen kididdiga da wayar da kan maniyatan aikin Hajjin Dokta Aminu Yammawa an samu halartar maniyatan a babbar Hedkwatar hukumar wanda ke alamta bude taron bitar ga sauran shiyyoyin hukumar dake fadin Jahar.
Wakilin ASKGLOC NEWS ya tuntubi wasu daga cikin maniyatan da suka halarci wannan taron bita don jin ta bakin su akan yadda ake tafiyar da shi. Wani maniyaci mai suna Abubakar ya ce, "abu na farko da na fara sani shi ne, kamar yadda muke ji malamai na fadi aiki ne wanda yake bukatar juriya da hakuri. Sannan aiki ne wanda yake da mataki-mataki ba kamar yadda nayi zato ba. Nayi tsammanin yin Dawafi da hawan Dutsin Arfat sune kawai aikin, ashe ba haka abin yake ba. Shi kan shi aikin ya kasu kashi uku, wanda ni da zanje a wannan bangaren zan fara da yin Umra kafin shi gundarin aikin. Sannan na fahimci, akwai batun ziyarar wasu muhimman wurare a garin Madina baya ga ziyarar kabarin fiyayyen halitta wanda da nayi zaton ziyara da ake cewa iyakar ta nan. Malam Abubakar yayi bayani mai tsawo akan irin abubuwan da ya fahimta ga aikin Hajjin saɓanin abin da yayi zato da farko.
Ita kuwa wata maniyaciya da ta ƙi fadin sunan ta, tace, "ashe akwai abubuwa da yawa da mu mata aka sauƙaƙa mana a wajen aikin saɓanin maza. Ba dole ne ba sanya Harami na daura gyale da mayafi ba gare mu. Sannan naji ance wajen yin dawafi da sa'ayi ba dole ne sai munyi wannan sassarfa ba. Akwai abubuwa da dama da naji mun samu saukin aiwatar da su ga aikin na Hajjin wanda nayi zaton komi na miji ya aikata sai nayi daidai da na shi. Gaskiya wannan bitar wani ilmi ne mai zaman kan shi wanda mutun zaiji tamkar ya gama aikin idan ya fahimci yadda yake",inji ta. Alhaji Muhammadu tsohon Alhaji ne, amma yace, a duk lokacin da Allah ya bashi ikon zuwa sabke farali, to bai bari wannan taron bita ya wuce shi domin sanin cewa, duk shekara ana samun wani bambanci ga aikin. "Muna samun bayanan wasu shirye-shirye ko tsare-tsaren da su hukumomi a kasar ta Saudiya take kawowa".
Wakilin namu har ila yau, ya shiga cikin sauran jama’ar gari don jin yadda suke kallon wannan taron bita da hukumar ke yi. Alhaji Ashiru mazauni acikin garin Katsina yace, "gaskiya hukumar tana bakin ƙoƙari wajen sabke nauyin da Allah ya aza masu. Babban abin da ba zan manta da shi ba shi ne, aikin Hajjin 2022 da ya gabata. Baya ga ƙarancin kujeru, an kuma samu wasu matsalolin musamman akan biza. Amma duk da kurewar lokaci, sai muka ji labarin cewa shi Daraktan hukumar ya ja wata tawagar sa zuwa Abuja don warware wasu matsalolin kuma kamar yadda muka ji yayi tafiyar a ranar daren ƙarshe, wato ana gobe za'a rufe filin jirage acan kasa mai tsarki, amma ya ƙarace ya tafi don warware matsalar wasu shi bai damu da kan shi ba saɓanin yadda muka samu labari a wasu jihohin inda jami'an suka yi tafiyar su suka bar wasu maniyatan acikin halin ko oho. Wannan abu ya burge ni, ya kuma ƙara tabbatar mana da cewa, suna aiki bilhaƙƙi da gaskiya. Sannan ya tsaya akan wannan tsari na wanda ya fara biya shi za'a fara ba kulawa. Wani abin ma da har yanzu nike jinjinawa hukumar shi ne, na mayarwa da majiyatan da suka yi wannan aiki na 2022 sauran wasu kudaden da aka samu rankon su. Ina tabbatar maka a baya can ba'a samu hakan ba domin babu wanda zaice maka an samu wani ragi balle ya baka".
Ita dai hukumar jin dadin Alhazan ta Jahar Katsina tana bayar da wannan horon faɗakarwa ga maniyatan jahar a duk lokacin da fara aikin Hajjin ya gabato domin maniyatan su tafi da ilmin aikin. Tana kuma gaiyato mabambantan malamai musamman daga ɓangaran Darika da Izala domin ilmantar da maniyatan yadda ake yin aiki da kuma abubuwan da ake bukatar maniyanci yayi ko kada yayi a lokacin da yake gudanar da aiyukan ibadar a can ƙasa mai tsarki. Irin wannan fadakarwa bata tsaya anan cikin gida ba, hatta da can ƙasar ana yiwa maniyatan matashiya wanda hakan yake sa maniyatan da suka fito daga Jahar Katsina suke shan bamban da saura a wajen gabatar da aikin da kuma bim doka da odar da aka sanar da su a kai. Hakan kuma na da nasaba da abin da yasa Jahar take samun yabo hatta daga can ƙasar ta Saudiya ba wai anan cikin gida kaɗai ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post