Ga jagororin alhazai "KU JI TSORON ALLAH - inji Sarakunan Katsina da Daura
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
An tunasar da shugabannin hukumar jin dadin alhazai ta Jahar Katsina akan nauyin jama'a masu zuwa aikin ibada a ƙasa mai tsarki da su yi iya ƙoƙarin su na ganin sun sabke wannan nauyi acikin nasara. Wannan tunasarwa ta biyo bayan kai ziyarar neman albarka da ƙarin shawarwari a yayin wata ziyara wadda Shugaban hukumar jin dadin alhazan na Jahar Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir wanda kuma yake shi ne Magajin Garin Katsina yayi jagorancin sauran membobin wannan hukuma da ake kira da "Board Members" a turance suka kai ziyara a masarautun Katsina da Daura, Maimartaba Dokta Abdulmuminu Kabir da Maimartaba Dokta Farouk Umar Farouk.
Shugaban hukumar a lokacin da suka ziyarci masarautun ya shaida masu cewa, sun ziyarce su ne a matsayin su na iyayen ƙasa kuma shuwagabannin al'umma domin neman tubaraki da kuma neman shawarwari ta yadda zasu gudanar da aikin su lafiya sun kuma sabke wannan nauyi na ibada wanda Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari ya aza masu.
Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar katsina Kuma Magajin garin katsina Alhaji Aminu Abdulmumini kabir Usman tare da sauran membobin shi sun Kai ziyarar Ban girma ga masu martaba sarki katsina da Daura Mai martaba Alhji Abdulmumini kabir Usman da Maimartaba Alhaji Umar faruq Umar.
Da yake Jawabi a masarautun guda biyu Shugaban Hukumar Alhaji Aminu Abdulmumini kabir Usman ya Shaida masu cewa sunzo masarautun ne Domin Neman tabarraki tare da Addu'ar su akan wannan Aiki da maigirma gwamna rt Hon.Aminu Bello masari ya basu. "Ina amfani da wannan dama in shaida cewa, tuni wannan hukuma ta himmatu wajen aiwatar da shirye-shiryen aiwatar da wannan aiki wanda bada jimawa ba za'a fara jigilar maniyatan zuwa ƙasa mai tsarki domin sabke farali. Daga cikin shirye-shiryen akwai yiwa maniyatan bitar yadda ake gudanar da aikin Hajjin. Wannan taron bitar an aiwatar da shi ko ana cigaba da yi a dukkan ofisoshin shiyyoyin da ake da su a fadin Jahar kuma ana samun nasara ta fahimtar maniyatan.
A jawaban da suka yi, Sarkin na Katsina Dokta Abdulmuminu Kabir da takwaran shi na Daura Dokta Farouk Umar Farouk bayan taya su murna da addu'a, masu Martabar sun ja hankalin shugabannin akan cewa, su zage dantse wajen aiwatar da wannan aiki mai muhimmanci wanda yana É—aya daga cikin shika-shikan musulunci. Sannan sun yi kira gare su da su ji tsoron Allah. Su sani cewa Allah zai tambaye su a ranar tambaya akan yadda suka aiwatar da wannan aiki. Aikin Allah ne, yana sa ido ga duk wanda yake aiwatar da shi domin shi ne mai yin sakaiya