CIRE TALLAFIN MAI TALAKKA KE SHAN WUYA - Alin ƙwai
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
Wani matashin ɗan kasuwa Alhaji Alin Ƙwai ya ja hankalin gwamnati mai zuwa akan da su yi taka tsan-tsan wajen batun cire tallafin mai da gwamnatin mai barin gado ta shirya yi wanda daga bisa ta jinginar da batun ga ita sabuwar gwamnatin mai zuwa. Alhaji Ali yayi bayani mai tsawo a wata hira da wakilin ASKGLOC NEWS a ofishin sa dake cikin garin Katsina, inda yayi matashiya akan cewa, "wannan tallafin ne kadai ɗan Najeriya ke amfana da shi daga kowane sashe na arzikin kasa. Mu dubi fannin wutar lantarki da sauran irin su, hatta da bangaren kiwon lafiya babu inda talakka ke samun sauki".
Matashin É—an kasuwar ya kawo misali hatta da batun kasuwanci inda kullun farashi hawa yake yi babu batun safkowa koda da rana guda duk da cewa akwai batun tallafin. To shin idan aka dauke shi ina mutumin dake cikin karkara zai sa kan shi? "Don haka, ina kira ga ita sabuwar gwamnatin tun daga matakin jaha har zuwa ga kasa, maimakon batun cire tallafi, su bi hanyar inganta rayuwar al'umma musamman batun kawo karshen matsalar tsaro wadda ita ce kan gaba. Sannan batun janyo masu sanya hannun jari da kafa kamfanoni da mayar da hankali wajen inganta noma, ba wai batun cire wani tallafi ba, kuma ga abin da ya zamo tamkar jini a cikin jikin mu, inji matashin.
Har'ila yau, Alin ƙwai ya tunasar da sauran al'umma cewar, cigaba da yin addu'o'in zaman lafiya da samun cigaban kasa ya kamata a mayar da hankali maimakon surutan da basu da wani amfani. "Mun roki Allah ya zaba mana mafi alheri, to ga sakamakon da muka samu wanda ya kamata ace mun rungumi hakan tare da bayar da goyon baya don cigaban kasar wadda bamu da wadda ta fi ta, inji Alhaji Alin Ƙwai.