ƘARAMAR HUKUMAR MANI ZATA ƊAGA DARAJAR ƊAKIN KARATU DA TA MALLAKA

ƘARAMAR HUKUMAR MANI ZATA ƊAGA DARAJAR ƊAKIN KARATU DA TA MALLAKA - Dr. Yunusa
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
(Dokta Yunusa shugaban ƙaramar hukumar Mani) 
Shugaban ƙaramar hukumar Mani Dokta Yunusa Muhammad Sani Bagiwa ya ce, karamar hukumar zata gyara tare da ɗaga darajar ɗakin karatu wanda ya zamo mallakin karamar hukumar domin tafiya daidai da zamani. Shugaban ya baiyana haka ne a wajen wani taron bita na yini guda wanda kwamitin Zakka da Waƙafi ya shirya ƙarƙashin jagorancin Sa'in Durɓi har ila yau Sa'in Hausa Alhaji Mustafa Abdullahi Bujawa ya shirya. Dokta Yunusa ya ce, "kamar yadda muka sani a can baya shi wannan ɗakin karatu mallakar gwamnatin jaha ne kuma an gina tun ana ƙarƙashin gwamnatin tsohuwar Jahar Kaduna. Tun a wancan lokacin babu wani amfani da al'ummar Mani ke yi. Ganin haka yasa na roƙi Maigirma Gwamna Masari da a gyara mana shi ko kuma mu a barmu mu gyara, bayan nuni da yayi akan cewa, wannan ɗakin karatu baya daga cikin irin waɗanda gwamnatin jaha zata gyara saboda yana daga cikin tsaffin ƙananan hukumomi. Ƙarshe dai na nemi alfarmar a mallakawa ƙaramar hukuma shi".
Kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya shaidawa mahalarta taron da kuma al'ummar Mani baki ɗaya, ɗakin karatun a yanzu ya zama mallakin ƙaramar hukuma bayan amincewar da Gwamnan yayi. "Saboda haka yanzu zamu gyara wannan ɗakin karatu tare da sanya mashi na'urorin zamani domin amfanin masu nazari da kuma bincike. Bisa wannan ne inda hali, nike kira ga su masu tattara wannan zakka da su riƙa fitarwa wannan sashi na neman ilmi wani abu domin ci gaba da inganta shi kamar yadda muka sauran takwarorin na wasu ƙasashen nayi. Har ila yau, Dokta Bagiwa ya ƙara neman wata alfarmar daga wannan kwamiti na su riƙa duba ɓangaren kiwon lafiya. Shugaban ƙaramar hukumar na Mani ya ce, sau da yawa za'a samu marassa lafiya masu bukatar agajin gaugawa amma saboda rashin kudi har sai su kai ga shiga cikin wani hali wanda a wasu lokuttan ma har a rasa rai. "Akan wannan nike sake roƙon wannan kwamiti na Zakka da Waƙafi da su riƙa ware wani kaso na daga cikin abin da suke tarawa don bayar da tallafi a irin wannan sashen.
(Durɓin Katsina Alhaji Umar Babani Isa) 
A nashi jawabin, Durɓin Katsina Hakimin na Mani Alhaji Umar Babani bayan jinjinawa wannan kwamiti musamman shi Sa'in Durɓin akan irin yadda yake tafiyar da aikin da aka aza ma shi, Hakimin ya baiyana wasu abubuwan da aka samu na sanarori akan su musamman akan abin da ya shafi fadakarwa na muhimmancin bayar da Zakka ga mabukata. Hakimin har ila yau, ya ce, "wannan aiki tun lokacin marigayi Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman ya bayar da umarnin aka su a dukkan fadin garuruwan hakimansa, amma tun wancan lokacin da aka kafa su babu wani abin da aka gani na zahiri sai dai fadin akwai su. To sai mu anan masarautar Mani Allah ya bamu ikon aiwatar da aikin wannan kwamiti ƙarƙashin jajircewar wannan bawan Allah wanda bai nemi a bashi wannan muƙami ba na Sa'i, Allah ne ya nufe shi da samun wannan rahama kuma yake aiwatar da aikin bakin iyawarshi.
Durɓin wanda yayi bayani mai tsawo akan aiyukan wannan kwamiti tun farkon kafa har zuwa yau, har ila yau, ya taɓo maganar jami'ar tafi da gidanka ta gwamnatin tarayya wadda aka gina a ƙaramar hukumar ta Mani amma babu wani abin da ake yi acikin ta. "A mafi yawan lokutta jami'ai na zowa akan batun wannan jami'a har muka gaza gane makomar ta, to sai yanzu muka ɗauki wani mataki na sanin matsayar jami'ar da kuma irin amfanar da zamu yi da ita. Allah cikin ikon shi, yanzu mun zauna da wasu jami'an kuma mun san inda aka dosa da abin da za'ayi a yanzu saɓanin abin da ke faruwa a baya.
Shi kuwa Sa'in Durɓin kuma Sa'in Hausa na farko, Alhaji Mustafa Abdullahi Bujawa yace, babu abin da zai yi illa godiya ga Allah da ya jarabce shi da wannan matsayi wanda yake yana ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar. Ya ƙara da cewa, "Bayan bani wannan muƙami abu na farko da na fara yi shi ne buga littattafai akan sanin mene ne Zakka da yadda ake fitarwa da bayar da ita ga mutane 8 kamar yadda Allah ya raba. Mun zagaya dukkan yankunan magaddai da masu unguwanni inda muka raba waɗannan littattafai domin ilmantarwa. Sannan kuma muka fara karbar wannan Zakka da mutanen da ya zamo wajibi su fitar da ita. Amma anan abin da muka riƙa yi shi ne, duk inda muka amshi wannan zakka to ba mu fitowa da komai daga wurin har sai in mun tabbatar da babu wadanda za'a ba wannan zakka kamar yadda Allah ya ce. To anan ne zamu fito da ita zuwa ga Hakimi domin sanin abin da za'a yi. Kafin wannan sai da muka rubuta sunayen duk wadanda suka cancanci fitar da zakkar wanda idan mutun ya ƙi bayarwa, to zamu ɗauki mataki kamar yadda addinin musulunci ya zo da shi". 
 (Alhaji Mustafa Bujawa Sa'in Hausa na farko) 
Sa'in Hausar na farko, ya sha alwashin da zarar Maimartaba Sarkin Daura yayi bikin naɗa shi, to daga wannan rana zai bi duk inda sarautar shi ta kai domin ganin cewa ya amso wannan zakka don raba ta waɗanda Allah ya ce a ba tare da gudanar da wasu aiyukan waɗanda aka amince da yin su daga cikin abin da aka tara. 

Post a Comment

Previous Post Next Post