AN HANA MASU SANA'AR KURKURA ZUWA BIKIN ƘAUYAWA A KATSINA

AN HANA MASU SANA'AR KURKURA ZUWA BIKIN ƘAUYAWA A KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Ƙungiyar masu sana'ar keke NAPEP ko ƙurƙura a Jahar Katsina ta kafa dokar yin amfani da ita a duk wani shagalin bikin da za'ayi wasa da na'urar musamman a wajen shagalin ɗaurin aure, ƙauyawa(Kauyawa party) ɗaukar amarya da sauran irin su. Shugaban ƙungiyar na Jahar Katsina Alhaji Jamilu Isyaku ne ya shaidawa wakilin ASKGLOC NEWS haka a ofishin sa dake Kofar Soro acikin garin Katsina.
"Daukar wannan mataki ya zama dole lura da irin yadda wasu daga cikin mutanen mu ke wasa da rayukan al'umma a irin waɗannan lokutta ba tare da la'ari da abin zai faru ba. Zaka mai sana'ar maimakon ya tattala abin neman abincin shi amma sai ya zamo yana mugun wasa da ita da sunan murnar biki. Saboda haka, daga yau wannan doka ta fara aiki a dukkan fadin jahar nan, sannan mun ba sauran shugabannin umarnin daukar ƙwaƙƙwaran mataki akan duk wannan aka kama ya karya dokar". Alhaji Jamilu yayi kira ga sauran jama'a musamman masu gaiyatar masu kurkurar don daukar jama'a a wajen sha'anin kowane irin taro da su kai rahoton duk wanda suka samu yana wasa da abin hawan ga hukuma mafi kusa.
Shi ma wani Basarake a ƙaramar hukumar Batagarawa Alhaji Muntaka Magaji Ɗanɗagoro yayi kira ga masu wannan sana'a ta ƙurƙura da cewa, hanya ce ta rufawa kai asiri ba wasa da rayuka ko dukiyar al'umma ba, don haka su riƙe ta da muhimmanci. Sannan su guji aikata duk wani abin da ka iya zama laifi ne walau a addinance ko a hukumance. "Jama'a na kallon irin yadda suke gudanar da harkokin su. Anan ina kira ga shugabannin su da suka daukar matakan bani ba sabo ga duk wanda ya aikata laifi. Sannan inda hali, su sanya masu dokar tashi daga aikin musamman idan dare yayi domin ko ba komi akwai kiwon lafiyar su da kaucewa fadawa hannun bata gari ko azzaluman mutane", inji Magaji Ɗanɗagoro Alhaji Muntaka Magaji. 

Post a Comment

Previous Post Next Post