AN FARA JIGILAR MANIYATAN JAHAR KATSINA

AN FARA JIGILAR MANIYATAN JAHAR KATSINA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Jirgin farko na kamfanin Max Air kirar Boeing 747 mai lamba 5N-ADM(1) ya fara jigilar maniyyatan Jahar Katsina da misalin karfe 3 da minti 6 na dare daga filin jirgin sama na Umaru Musa 'Yar'aduwa dake cikin birnin Katsina zuwa ƙasa mai tsarki.
Jirgin ya dauki maniyatan da suka fito daga shiyyar Daura da suka hada da kananan hukumomin Baure, Daura, Mai'aduwa, Sandamu da Zango.
Sauran maniyatan sun fito daga karamar hukumar Bindawa dake shiyyar Mani.
A jawabin shi na bankwana ga maniyatan, Amirul Hajji na wannan shekara wanda kuma shine Kakakin Majalisar Dokoki na jahar Katsina Honarabil Tasi'u Maigari Zango wanda ya jagorancin kwamitin aikin Hajjin ya ce, "Alhazanmu na Jahar Katsina muna yi maku fata, muna yi maku addu'a Allah ya kai ku lafiya a kuma gama lafiya. Muna yin kira a gare ku cewa acikin jirgin nan akwai malamai wadanda zaku tafi tare da su. Don Allah idan anje tun daga Jidda ba Makka ko Madina ba, duk abinda ka gani wanda baka fahimta ba domin tafiya ce ake yi ta addini, to ayi tambaya". Amirul Hajjin har ila yau, ya sake yin kira ga maniyatan akan cewa, idan anje a sanya Jaha da kasa baki daya addu'ar samun zaman lafiya tare da irin halin da ake ciki. Ya tunasar da su kan zama jakadu na gari wajen yin biyayya da da'a acan kasa mai tsarki ta yadda duk inda aka je a san cewar wadannan alhazan jahar Katsina ne.
Shi ma da yayi na shi jawabin, Babban Daraktan kwamitin hukumar jin dadin alhazan Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ya ce, "kamar yadda kuka sani, anyi sama da wata guda ana yi maku wa'azi da kuma bitar yadda ake yin aikin Hajjin, to ku yi kokarin ganin cewa kunyi amfani da abubuwan da kuka koya. Sannan ku sani akwai ma'aikatan hukumar alhazan da suke tare da ku domin yi maku jagora tun daga Jidda har zuwa Madina da kuma Makka ta yadda ba zaku fuskanci wata matsala ba da iznin Allah". Daraktan kwamitin a madadin Gwamnan Jahar Malam Umar Dikko Radda, yayi addu'ar sabka lafiya tare da neman yiwa jaha da kasa addu'a. "Ku sanya sabbin shugabannin mu cikin addu'ar Allah yayi masu jagora, su yi mana mulki acikin adalci. Nan da 'yan kwanaki kadan muna nan tafe zamu same ku da yardar Allah. Daga cikin tawagar da suka yiwa maniyatan bankwana har shugaban kwamitin aikin Hajjin Maigirma Magajin garin garin Katsina Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir da sauran wasu membobin kwamitin. Jirgin na farko na kamfanin Max Air ya tashi da maniyata 543 da kuma jami'ai 4 domin zuwa kasar Saudiyya inda zai ratsa ta kasar Nijer zuwa kasar Libya da kasar Masar ya tsallake ruwa don shiga kasar ta Saudiyya. Wannan zagaye ya biyo bayan rufe sararin samaniyar kasar Sudan sakamakon yakin da suke yi. Ana zaton maniyatan zasu dauki kimanin sa'o'i 6 zuwa 7 maimakon awa 4 zuwa 4 da rabi kafin sabkar su a filin Abdul Aziz dake Jidda 

Post a Comment

Previous Post Next Post