Aikin Hajji 2023 - GWAMNATIN JAHAR KATSINA KE CIYAR DA MASU TARON BITA

Aikin Hajji 2023 - GWAMNATIN JAHAR KATSINA KE CIYAR DA MASU TARON BITA 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 
    E D Alhaji Sulemain Nuhu Kuki 

Mahalarta taron bitan sanin yadda ake gudanar da aiyukan Hajji wanda hukumar Jin dadin Alhazai ta jahar Katsina suke gabatarwa a shiyyoyin hukumar dake fadin Jahar wanda gwamnatin Jahar Katsina ta dauki nauyin gudanarwa, sun yaba da irin yadda ake gudanar da taron bitar. Kazalika, mahalarta taron sun jinjinawa gwamnatin jahar karkashin jagorancin Gwamna mai barin gado Rt. Aminu Bello Masari wanda a karkashin jagorancin shi ne aka shirya wannan taron bitar. Wasu daga cikin jinjinawa gwamnatin jahar da mahalarta taron bitar suka yi sun hada da ciyar da su da ake yi a lokacin da duk suka halarci taron, kamar yadda wasu da aka zanta da su a wasu shiyyoyin da ake gudanar da taron.
     Sashen maza a wajen taron bitar 

Kamar yadda wata sanarwa ta fito mai É—auke da sa hannun Jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ya sanyawa hannu tace, dukkan wuraren da jami'an hukumar jin dadin alhazan ta ziyarta don ganin yadda taron bitar ke gudana, baya ga yabo da ake samu babu wani wuri inda aka samu korafi. Anan hukumar karkashin Babban Daraktan ta Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ta yabawa masu aikin gudanar da taron bitar da suka hada da jami'an shigi da fici, jami'an hana fasa kwabri da takwarorin su na hana tu'ammali da miyagun kwayoyi, jami'an 'yansanda da na kiwon lafiya da sauran masu ruwa da tsaki a wajen gudanar da aikin Hajjin.
 
   Sashen mata a wajen taron bitar 

Alhaji Karofi acikin sanarwar yace, daga cikin shiyoyin da jami'an hukumar suka ziyarta domin duba yadda ake gudanar da taron bitar sun hada da shiyyar Daura da shiyyar Funtuwa da shiyyar Kankiya da kuma shiyyar Katsina. "Abin da ya kara burgewa a wajen wannan taro shi ne, irin yadda mahalarta taron suke sauraren abin da ake gaya masu acikin natsuwa da kuma yin tambayoyi akan duk wani abin da basu gane ba. Wannan ya nuna suna shirye da yin aikin kamar yadda yake tare kuma da yin nuni akan kiyaye doka da oda tun daga nan gida har zuwa kasa mai tsarki. Fatan mu Allah yasa ayi aiki lafiya kuma a gama lafiya, tare da dacewa". Wannan taron bitar kamar yadda aka yi hasashe, na daga cikin matakan samun nasarar aiwatar da aikin Hajjin da jahar ta Katsina tayi fice akan shi wanda yake kara janyo mata tagomashi da samun yabo daga gida kuma can kasar Saudiya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post