442 BAYAN SHARE WATANNI 6 A TSARE GIDAN YARI ZA'A BAYAR DA BELIN SHI A NIJER

442 BAYAN SHARE WATANNI 6 A TSARE GIDAN YARI ZA'A BAYAR DA BELIN SHI A YAMAI
Daga Kabir Ahmed S/Kuka

Mawaƙin Gambarar zamanin nan Mubarak wanda aka fi sani da suna 442 wanda yake tsare a gidan Yari a birnin Yamai ta Jamhuriyar Nijar kimanin watanni shidda da suka wuce, bisa zargin yin sojan gona ta hanyar yin fasgo na ƙasar ta Nijer bayan bada bayanan ƙarya akan cewa ɗan ƙasar ne ta hanyar yin takardun haihuwa na bogi da nufin fita ƙasashen Turai, wanda hukumomi a ƙasar suka gano shi a lokacin da yaje filin sabkar jiragen sama dake cikin babban birni bisa yunƙurin na shi na fita.
A yanzu haka shirye-shiryen bayar da shi belin sun yi nisa. Hakan ya biyo bayan kai gwauro da mari da mahaifiyar shi ta riƙa yi na neman sa bakin masarautu biyu, wato masarautar Kano da kuma ta Damagaram. Kamar yadda ASKGLOC NEWS ta kalato, mun samu rahoton cewa, hatta da ƙungiyar 'yan wasa ta garin na Yamai ɗin sai da suka shiga batun kafin daga bisa ofishin Jakadancin Nijeriya ta shiga cikin batun bayan zurfafa binciken da ofishin yayi akan lamarin. Rahotanni da muka samu na cewa mahaifiyar har kokarin daukar wata ƙaramar lauya ta yi domin neman wannan beli wanda daga bisa aka ce ofishin na jakadanci ya bayar da wani babban lauya akan lamarin wanda hakan ya samar da filin tattaunawa don samun belin. Kamar yadda labari ya iske mu, ita mahaifiyar ta Mubarak ta kwashe sati biyu acikin garin na Yamai wajen fafutukar ganin an saki ɗan nata.
Indai za'a iya tunawa, shi dai 442 yayi yunƙurin yin amfani da takardun na ƙasar Nijer maimakon na shi na Najeriya domin fita ƙasashen turai. Tafiyar da in baya ga shi da abokin tafiyar babu wanda zai iya baiyana gaskiyar manufarta. Wasu na cewa, tafiyar zuwa turai na da nufin neman suna ta hanyar sana'ar su ta waƙar gambara da ake kira "Hip Hop" yayin da wasu ke cewa tamkar yin hijira mai neman mafaka a wata ƙasa ganin irin yadda suka fara samun matsala don gane da irin yadda suka ɓullo da nasu irin salon na wannan waƙa tare da 'yar wasan kwaikwayon nan wadda ta canza daga wasan zuwa waƙar gambarar mai suna Safara'u, wato, Safa kamar yadda take ambatawa acikin wata waƙar ta da take cewa, "na canza kala, na bar sana'ar 'yan wahala. Safa Safa Safara'u". Sai dai abin da mafi yawan jama'a ke tambaya akan alaƙar ita Safara'un da shi 442 shin ta yanke ne da har yayi wannan yunƙurin tafiya bada ita ba? Me yasa har yanzu ba'aji tace uffan ba game da kamun da kuma tsarewar da aka yiwa shi abokin waƙar wanda yake jagorancin ƙungiyar ta su, wato, 442?

Post a Comment

Previous Post Next Post