2023 Ranar 'Yancin ' yan jaridu - YA KAMATA A BA 'YAN JARIDA KULAWA TA MUSAMMAN A JAHAR KATSINA

2023 Ranar 'Yancin 'yan jaridu - YA KAMATA A BA 'YAN JARIDA KULAWA TA MUSAMMAN A JAHAR KATSINA 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 
Ƙungiyar 'yan jaridu NUJ ta Jihar Katsina ta mika sakon taya murna ga ‘yan jaridu da sauran kwararru a harkar yada labarai, dangane da ranar ‘Yanci ‘Yan Jarida’ ta bana.
 Majalisar Dinkin Duniya ce ta kebe wannan rana domin wayar da kan al'ummar duniya kan muhimmancin aikin jarida da kuma baiwa dukkan 'yan kasa damar fadin albarkacin bakinsu. Kamar kowace shekara, Taken bikin na bana shi ne "Sanya Makomar 'Yancin fadin albarkacin baki a matsayin Jagora na sauran 'yancin dan Adam".
A sakon da bayar dangane da bikin wannan rana, Shugaban Ƙungiyar 'yan jaridu na Jahar Katsina Kwamared Tukur Hassan ÆŠan Ali ya ce, "muna kira ga takwarorinmu, ’yan jarida a Jihar Katsina, da su ci gaba da bin dokoki da ka’idojin aikin jarida a duk inda suka muka samu kan mu don aiwatar da aikin. Mu ci gaba da kasancewa masu tsoron Allah da kishin kasa wajen gudanar da ayyukanmu.  
"Mu tuna cewa ’yan jarida sun taka rawar gani wajen fafutuka da samun ’yancin kai na Nijeriya a shekarar 1960, da kuma dawowar dimokuradiyyar da ake yi a yanzu tun daga 1999 zuwa yau.
 Haka kuma, a jihar Katsina, alÆ™alumma sun nuna cewa ba karamar gudummawa 'yan jaridu suka bayar ba wajen ci gaban jihar ta hanyar bayar da rahotanni masu kyau da suka shafi harkokin mulki ga sauran al’umma a jihar.
 Don haka kungiyar ta NUJ a matsayinta na kungiya tana da ra’ayin cewa ‘yan jarida a matsayinsu na hudu na wannan mulki ya cancanci gwamnati da sauran al’ummarmu su ba su kulawa sosai.
Kwamared ÆŠan Ali ya ce, "Mun yi nadama kan yadda akasarin ‘yan jarida ba su da albashi, ba su da kayan aiki da kuma rashin kuzari musamman ‘yan jarida masu zaman kansu. Don haka muna kira ga duk masu mallakin kamfanonin yada labarai na bugawa da watsa shirye-shirye da su ba da fifiko ga jin dadin ma’aikatansu cikin gaggawa". 
 Dangane da kalubalen tsaro da ke fuskantar jihar Katsina da sauran jihohin da ke makwabtaka da ita, NUJ a shirye take ta ba da hadin kai ga dukkan Hukumomi musamman bangaren tsaro domin shawo kan matsalar.
 A daidai lokacin da gwamnatin Jiha mai ci ke shirin mikawa zabbar sabuwar gwamnati mai jira, muna fatan fahimtar juna da ke tsakanin ‘yan jarida da gwamnatin Jiha mai barin gado ta tabbata a hannun gwamnati mai zuwa domin ganin cewa, aikin na jarida ya kara ingantuwa acikin jahar ta Katsina, inji shugaban kungiyar 'yan jaridun na jaha NUJ Kwamared Tukur Hassan Dan'Ali. 

Post a Comment

Previous Post Next Post