ZAN YI IYA KOKARI NA DON KAWO CIGABA A KARAMAR HUKUMAR MANI - Bujawa

ZAN YI IYA KOKARI NA DON KAWO CIGABA A KARAMAR HUKUMAR MANI - Bujawa
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Zababben dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Mani a Jahar Katsina Honarabil Shu'aibu Zaiyana Bujawa yace, zasu yi wakilci bisa adalci tare da yin duk wani abin da ya kamata domin ganin sun kyautata jama'a musamman karamar hukumar da yake wakilta. Akan haka ya nemi jama'ar karamar hukumar da cewa, yana da kyau su fara fahimtar su da kuma abin da suke shirin yiwa karamar hukumar. Kamar yadda Honarabil Shu'aibu ya ce, "in jama'a ba su fara fahimtar mu ba, to zaiyi wuya su gane abin da zamu yi masu." Duk inda suka ga mun yi masu ba daidai ba to su yi magana domin kofa ta a bude take kowane lokaci na sauraren jama'ar da nike wakilta. Tabbas ina da kudurori da yawa da zan gabatarwa majalisa da zarar mun fara zama, musamman matsalolin da jama'a ta ke fuskanta. Zan yi kokarin ganin cewa, an sanya duk wani kudurin da na kawo wanda zai shafi kudi cewa an sanya acikin kasafin kudin da majalisar zata amince da shi a kuma je a aiwatar da kowane irin aikin ne ga su al'ummar karamar hukumar ta Mani"
Zababben danmajalisar ya kara da cewa, wasu aiyukan da ba na majalisa ba ne amma za'a iya samun su don cigaban al'umma, to zaiyi iya kokarin shi na ganin cewa ya samo irin wadannan aiyukan musamman wadanda ke fitowa daga wasu kungiyoyi na duniya. "Zan taimaka a wajen bayar da tallafin karatu saboda muhimmsncin ilmi, sashen sana'o'i da kasuwanci domin samar da abin dogaro da kai a tsakanin matasa. Abin da ya shafi bangaren kiwon lafiya dama kafin zabe akwai wasu shirye-shirye da muka fara yi wanda kuma a yanzu bisa yardar Allah zamu cigaba da su. Akwai batun harkokin noma da sauran su.
Honarabil Shu'aibu ya jinjinawa al'ummar ta karamar hukumar Mani saboda irin hadin kan da suke da shi musamman rashin samun wata tashin - tashina a tsakanin juna, sannan akwai biyayya ga shugabanni. "Sai dai anan sanin kowa ne cewar babban ƙalubalen da jama'ar suke fuskanta shi ne, batun matsalar ruwa. Anan bisa yardar Allah duk da saukin da ake samu a yanzu, wannan ba zai hana mu cigaba da lalubo wasu hanyoyin da zamu kawo karshen wannan wannan matsala ba wadda ta dade tana ci mana tuwo a kwarya. Akwai ma batun makarantar gaba da sakandire wadda ita in sha Allahu nike fatan kafin wa'adin zamana a majalisar ya kare, inga an samu wannan nasarar wadda aka fara tuga ta a yanzu.
Honarabil Shu'aibu Zaiyana Bujawa ya kara yin kira ga jama'ar karamar hukumar Mani da su cigaba da gudanar da duk wasu dabi'un da aka san su da su na alheri. Sannan su cigaba da bin doka da oda tare da yin addu'o'in samun nasara akan duk wasu aiyukan cigaban da aka kuduri a yankin. 

Post a Comment

Previous Post Next Post