Ƙidaya 2023 - AN KADDAMAR DA KWAMITIN MUTANE 24 DON WAYAR DA KAN AL'UMMA A KATSINA

Ƙidaya 2023 - AN KADDAMAR DA KWAMITIN MUTANE 24 DON WAYAR DA KAN AL'UMMA A KATSINA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 
   
Dangane da batun fara shirin kidayar jama'a da za'a fara a sati mai zuwa, hukumar kidaya jama'a ta kasa hadin guiwa da gwamnatin jahar sun kafa wani kwamiti domin wayar da kan al'umma akan muhimmancin yin wannan kidaya wadda ta hada har da gidaje. 
Kwamitin karkashin shugaban Mataimakin Gwamnan Jahar QS. Mannir Yakubu na da wakillai daga bangarori daban da suka hada da masarautun Katsina da na Daura, wakillai addinai, ƙungiyoyin farar hula, wakillan kafofin yada labarai na jaha da sauran masu ruwa da tsaki akan lamarin. 
A jawabin shi a wajen kaddamar da kwamitin, Kwamishinan hukumar Kidayar na kasa dake nan Jahar Katsina, Injiniya Bala Almu Banye yace, babban makasudin yin wannan kidaya ba wai kawai don a kawo sahihin jadawalin al'umma ba, kidayar na da nufin kawo abubuwan da zasu ciyar da kowane bangare gaba acikin al'umma musamman ta fuskar tsare-tsaren cigaba da kuma sanin yadda za'a tunkari wasu matsaloli idan sun ta so. 
Don haka, hukumar ba zata bar wani sashe ba a wajen tattara bayanai ta hanyar yin amfani da hanyoyi da kuma na'urorin fasahar zamani domin ganin cewa kwalliya ta biya kudin sabulu akan samar da karbabben sakamakon kidayar da za'a yi. Kwamishinan yayi jawabi mai tsawo akan irin shirye-shiryen da hukumar tayi don ganin cewa, an wayar da kan jama'a kuma sun karbi yin wannan kidaya hannu bib-biyu ta hanyar bayar da hadin kai don ganin an kidaya su daga kowane lungu da sako. 
Kamar yadda Kwamishinan yace, tuni aka yi kidayar gwaji a wasu kananan hukumomin da suka hada da Dutsi, Kurfi, Kusada da kuma Funtuwa a shekarar 2021. Sannan an sake yin wani a shekarar 2022 acikin watan Yuni a karamar hukumar Daura. Akan haka, yayi kira ga membobin wannan kwamiti akan kada su yi kasa a guiwa wajen fadakar da al'umma don ganin anyi wannan kidaya wadda yayi nuni da cewar ita ce ma'aunin da zata sa a san irin aiyuka ko tallafin da za'a ba yanki. 
A na shi jawabin, shugaban kwamitin kuma Mataimakin Gwamnan Jahar Katsina QS Mannir Yakubu ya fara da tunasarwa akan waccan kidaya da aka yi kimanin shekaru 17 da suka wuce, wato, a 2006 inda Jahar Katsina ta zo a matsayi na hudu a wajen yawan jama'a, wadda take da mutane sama da milyan 5 da dubu dari 8 da 1 da dari 5 da 84(5,801.584). Don haka akan wannan kidayar al'umma da kidaje da za'ayi ta kasa ta shekarar 2023 yasa gwamnatin Jahar tayi wasu kwamitoci guda biyu domin ganin cewar an samu nasarar wannan kidaya. Kwamitocin sun hada da na dabarun tsaro a lokacin aiwatar da kidayar da kuma kwamitin wayar da kan al'umma akan sha'anin kidayar. Ana sa ran kwamitocin zasu gudanar da aiyukan su kamar yadda aka tsara don gudanar da kidayar ta 2023 a matakin jaha da kananan hukumomi bisa nasara. 


Post a Comment

Previous Post Next Post