Hajj 2023 - "MUNA NAN AKAN TSARIN WANDA YA FARA BIYA.... PWB Katsina

Hjj 2023 - "MUNA NAN AKAN TSARIN WANDA YA FARA BIYA.... PWB Katsina
Daga Kabir Ahmed S/Kuka

     Alhaji Sulemain Nuhu Kuki Babban Daraktan PWB na Jahar Katsina 

Bayan hukumar alhazai ta ƙasa ta bayar da sanarwa yawan kudin aikin Hajji na 2023 na naira milyan biyu da dari tara da goma sha tara(N2.919.000) wasu jihohin kasar nan wanda jahar Katsina na daga cikin su, kamar yadda jami'in hulda da jama'a na hukumar jin dadin alhazwi na Jahar Katsina Alhaji Badaru Bello Karofi ya tabbatarwa ASKGLOC NEWS a Katsina.
Ƙarƙashin jagorancin Babban Daraktan hukumar na Jaha Alhaji Sulemain Nuhu Kuki, "hukumar na nan bisa tsarin ta na wanda ya fara biya shi ne wanda za'a fara baiwa kula. Saboda haka, maniyatan da suka bayar da kudin ajiyar su na naira milyan 2 da dubu dari 5 da suyi kokarin cika naira dubu dari 4 da 19 kafin 21 ga wannan wata na Afrilu, 2023, ranar da aka aiyana ta karshe domin karbar kudin aikin Hsjjin. Haka, suma wadanda can baya suka bayar da ajiyar naira milyan guda da rabi da su yi kokarin cikawa kafin wannan rana. Kazalika, hukumar ba zata karbi tsabar kudi a hannu ba, ana biya ne ta hanyar bankuna. Sannan maniyatan zasu biya cikon kidaden ne a ofisoshin hukumar dake shiyyoyin Jahar".
Farashin kujerun aikin wannan shekarar ya karu ne saboda tashin gwabron zabo da abubuwa ke ta yi a fadin duniyar, sannan ga farashin canjin kudi na kara hawa. Kazalika, hatta da farashin man da jiragen saman ke amfani da shi yayi tsada fiye da kima bayan ƙarancin shi da ake fama da shi. Har'ila yau, a can ƙasa mai tsarkin ma haka farashin abubuwa ke ta tashi kusan a kullum. Kadan daga cikin su harda maganar masabkan maniyatan da kuma farashin ababen hawan da ake amfani da su wajen hidimar maniyatan.
Hukumar jin dadin alhazan na Æ™ara kira ga maniyatan da suyi kokarin tsare wannan lokaci da aka bayar don karbar cikon kudin domin ba za'a sake karbar kudin kowa daga wannan rana sai fa in an sake samun wani karin lokacin daga ita hukumar alhazan ta Æ™asa. Ana dai sa ran za'a fara jigilar maniyatan aikin Hajjin wannan shekara daga ranar 21 ga watan Mayu, 2023. "A yanzu haka dai hukumar na cigaba da shirye-shiryen fara gudanar aikin wanda ya hada har da taron bita ga maniyatan da sauran hidimomin aikin. A karshe hukumar na Æ™ara shaidawa maniyatan cewar, kamar yadda ta saba, a wannan shekarar ma ta kamawa maniyatan masabkai kusa da Harami. 
A wannan shekarar jiragen Max Air da Air Peace da Azman da Flynas ne zasu yi jigilar maniyatan sama da dubu dari da suka fito daga fadin Æ™asar. Jiragen Arik da Value Jet ne zasu yi hidimar masu tafiya a tsarin da ake cewa, 'yan jirgin yawo'. 

Post a Comment

Previous Post Next Post