AYI HATTARA DA LABARAN SOSHIYAL MIDIYA

AYI HATTARA DA LABARAN SOSHIYAL MIDIYA - Sheikh Goni

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
Anyi kira ga al'umma musamman masu amfani da kafofin sadarwar zamani da su riƙa kawar da idanun su tare da liƙe kunnuwansu akan yadda ake yaɗa wasu labaran acikin wannan kafa. Matashin malamin addinin musuluncin nan Sheikh (Dokta) Goni Muneer Ja'afaru yayi wannan kiran a ranar asubucin nan a wajen tafsirin Al Ƙur'ani Mai Girma na watan Azumin da ya saba yi a duk shekara. Shehin malamin ya ankarar da masu nuna damuwarsu akan irin yadda suke yi a duk lokacin da suka ji ko suka ga wani baƙon abu.
"Duk mutumin da kasan baya fadin abu mai kyau akan tun can baya, to kada kayi zaton zai fadi wani abin da zaka ji dadin shi anan gaba. Da ma abin da baka son ne zai fadi a kowane lokaci. Saboda haka, kawai da kunnuwa da idanu akan ire-iren labaran shi ne mafi alheri fiye da yin wata maganar da kasan da ma mai wancen zance ya saba yin munanan kalamai akan ka". Shehin Malamin yayi wannan bayani a daidai lokacin da yake bayani a cikin kissar Annabi Yusuf akan irin kalaman da 'yan-uwan Annabi ke yin bayani akan shi ga fataken da suka tsince shi acikin rijiya.
"Yi ko jiɓanta wasu kalamai ga irin mutanen da Allah ya keɓe ya kuma basu wata matsaya da martaba acikin al'umma ba karamin kuskure ba ne". Acikin bayanan da yayi, malamin har ila yau, yayi kira ga mawaƙan zamani da su riƙa sanin kalaman da zasu riƙa amfani da su ga fiyayyen halitta ba wai ga wasu mutanen ba can daban.
Indai za'a iya tunawa, a 'yan kwanakin al'ummar musulmi suna ta baiyana ra'ayoyin akan wasu kalamai da wani malami da kuma wani É—an fim yayi acikin waÆ™a akan Manzon tsira, inda kowane yayi furucin cewa, baya bukatar taimakon Annabi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post