ANA YAƊA BAƘIN DODONNIN WAYA KO BAƘIN NEMAN KUƊI? Bincike

ANA YAƊA BAƘIN DODONNIN WAYA KO BAƘIN NEMAN KUƊI? -  Bincike

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 
               Jadoo acikin fim Koi mil Gaye
'Yan kwanakin nan an riƙa baza wasu hotunan da ake kira "Aliens" a turance, wato, "Baƙin abu ko Baƙin halittu". Waɗannan halittu masu kama da mutane a kafafen sadarwar zamani. An riƙa baza waɗannan hotuna ta siga iri biyu, wato, hoto maras motsi da kuma bidiyo. Sannan masu baza waɗannan hotuna suna ikirarin baiyanar su a wasu garuruwa ko jihohin Najeriya, kazalika, suna baiyana cewar, waɗannan dodonnin kamar yadda muka ga ya dace mu kira su da su, "yanzu suka sabka a wuri....kaza da kaza. Har ma wasu suna haɗawa da yin rantsuwar sabkowar su daga sararin samaniyar da ake kira," Mars".
Shin ko gaskiya ne akwai waɗannan halittu kafin batun baiyanar su?
Hakika, Allah Maɗaukakin Sarki ya baiyana mana cewar, yayi halittu iri-iri, waɗanda kuma ya ajiye su a mabambanta wurare da yanayi. Kaɗan daga cikin misalin wuraren zaman halittun da Mahaliccin ya halitta sun haɗa da cikin ruwa, ƙarƙashin ƙasa, bisa doron ƙasa da kuma cikin samman da ya halitta. Wasu ma acikin iska suke rayuwa. Yayi wasu a matsayi ko kamannu dabam-daban. Manya daga cikin su sun haɗa da dabbobi, ƙwari da tsuntsaye baya ga itatuwa da ciyawu da sauran su. Ya kuma baiyana cewar, wasu ma daga cikin halittun shi kaɗai ne yasan su da kuma inda ya ajiye su.
To su waɗannan "Aliens" ko Baƙin halittun da ake yaɗa hotunan su a yanzu suna cikin irin waɗancan halittu da Allah ya baiyana mana cewar shi yasan inda suke? Duniyar "Mars" kamar yadda ake cewa, masu binciken sararin samaniya sun baiyana hasashen su akan wannan duniya wadda Allah yayi da sauran irin ta, shin da gaske ne daga nan suke? Incan ne suke, to me ya fiddo su yanzu har suke sabkowa wannan duniya wadda take mazaunin mutane, aljannu da ruwa da wasu halittun? Shin suna ma daga cikin halittun da zasu zo daga cikin alamun ƙarshen duniya? Malam(Dokta) Aminu Yammawa ya shaida mana cewar, halittun da Allah ya baiyana cewar zasu zo a wajen ƙarshen duniya sune "Wajuju da Majuju". Su kuma gajeru, kuma da zarar sun baiyana to cin komi suke yi ciki harda mutanen. Sai kuma Taguwar Annabi Salihu tare da sake baiyanar Annabi Isa bayan Dujal. Su kuwa Aljannu da Allah ya basu damar rikiɗa ta kowave irin suffa, Allah bai baiyana su a haka har kuma su riƙa tsaya da yawa acikin mutane ana ɗaukar hotuna da su.
KWAIKWAYON BASIRI "(ARTIFICIAL INTELLIGENCE (AI)"
Kwaikwayon basirar halitta, wata fasaha ce ta Butun butumi (Robot) da aka kirkira wacce na'ura mai kwakwalwa ke sarrafawa. An kirkire ta ne domin saukakawa mutane neman ilimi, wasu lokutta ta kan yi bayani kamar yadda mutum kan yi. Har ma zai iya zana hasashe na mutum ko ya juya kalma zuwa hoto ko hoto zuwa kalma. 
Saboda haka ana son ayi amfani da wannan labari na kazon kurege dan a samu a cimma wata manufa wacce bamu san micece ba. Har yanzu wadanda suka kirkiri waccan fasahar zanen  AI basu gyara wannan zanen butun butumi ta yadda zai bayar da cikakken fasali na mutun ba, sai dai ko nan zuwa gaba. 
Saboda haka idan muka lura zamu gane cewa zanen "AI" Robot ne kawai, ba komi ba. A duba irin hotunan wadannan dodon wayar dake ta yawo a Facebook da sauran su, zaku ga basu da ainahin siffar "Aliens" da su mutanen kimiyar suka ce wai jirgin su ya taɓa sabka a wata unguwa a garin Bauchi a wasu shekaru can a baya. Sannan halayyar wadannan da ake turo bidiyo da hotunan su ba daya bace da ainahin Aliens da ake cewa na gaskiya ne. Kazalika, su wadancan bakin hallittu dake shigowa daga Sararin samaniya, kamar yadda ake nunawa a shirin fim(domin ko su da ake cewa acikin shirin fim ne ake nuna su) suna amfani da haske.
Bari mu dauki misalin wani fim na Indiya mai suna, "KOI MIL GAYA" acikin shi an warware mana hasashen da ake yi akan  wadannan bakin halittu. 'Jadoo' wanda ma'anar wannan kalma kamar yadda aka nuna ita ce, Haske. Acikin shirin wannan fim, an nuna yadda ake isar da sakon sauti ko tafiyar sauti daga wani wuri zuwa wani wurin. Ko tafiyar sauti daga wata nahiya zuwa wata ta hanyar hadin na'ura mai kwakwalwa. Ta hanyar aika wannan sakon sauti ne yayi sanadiyar gaiyato su wadannan bakin halittun da ake kira, ALIENS. Ba zan kawo bayanin abin duka baki daya ba, sai dai a takaice. Lokacin da sakon sautin ya isa cikin wata duniyar da ta zamo mazauna wadannan halittu masu amfani da haske, sun amsa wannan sakon kira wanda ya zamo masu tamkar gaiyata. "OUM" shi ne sunan sautin da aka yi amfani da shi. Lokacin da su wadannan halittu zasu shigo garin da aka yi amfani da wannan sauti, sai da duk wani abu mai amfani da haske ya tsaya cik sai hasken jirgin su kawai dake sabkowa kasa a hankali. Zamantowar su matsorata ga duk wata halittar dake cikin wannan duniyar tamu, yasa ganin Giwa acikin dajin da suka sabka, suka yi tashin gaugawa domjn komawa inda suka fito. A kokarin tashin ne suka bar wani daga cikin su. Wannan halitta ya fada hannun mutane, wanda kuma yake da karfin sarrafs abubuwa amma ta hanyar amfani da haske.
Har'ila yau, zamu iya tuna da shirin wakar Machel Jacson "Thriller". Mun ga yadda aka shirya yadda Fatalwa ke fitowa daga cikin kaburra. Mun gw fim na X-Men, Avatar I-Robot, MIB(Men In Black) da sauran su. Idan muka dawo a tsakanin mu, wato, abin da yake a fili ba ashirin fim ba, mai shekaru 50 wanda yake zaune ko alaka da mutanen mu na cikin Karkara, muna da masaniyar wani abin da ake kira, "KANBULTU" wanda ake yin shi ta hanyar sihiri, inda mutun yake canza halitta zuwa alamun Kura don tare hanya don yin sata ko tsorata matafiya cikin dare don a kwashe masu kayan da suka zubar don tsoro.
Kamar yadda wasu suka aza wasu tambayoyi akan wadannan hotuna da ake yadawa, shin da farko, wanene yake daukar wadannan hotuna, shin su ne da kan su ko kuwa? Shin sun shigo cikin wannan duniyar a yanzu inda suka rararrabu ko kuwa yau in sun sabka nan gobe sai can, sannan wa ke bayar da sanarwar sabkar su ko zuwa inda suka je. Ance suna da tsoro, ta yaya har ake daukar hoton su da mutane? A karshe Ustaz Muhammadu ya gargadi jama'a da su kiyayi janyowa kan su masifa wadda idan ta shigo bata da magani. Kazalika, yayi kira da akiyaye tayar da hankulan al'umma ana sanya masu tsoro acikin zukata musamman acikin wannan wata mai alfarma karshe yayi gargadi mai karfi akan yada karya.
HANYAR NEMAN KUDI CE
Sai dai wani bayanin da muka samu akan nuna wadannan hotuna da bidiyo da wasu ke yi na bakin halittu, wata hanya ce ta samun kudi ta yanar gizo da ake yi daga wasu kafofin sadarwar. Kamar yadda wani matashi wanda ya nemi a sakaya sunan shi yace, "abin da mutun ke bukata in ya aza wani hoto ko bidiyo shi ne samun masu yin sharhi ko sha'awa(comments da likes) saboda samun hakan, wata kaface da su masu kafafen suke gabatar da tallace-tallacensu na wasu kamfanonin da suka basu talla. Dama ai bukatar mai talla jama'a su san da shi. To mai aza irin wadannan hotunan wanda ke jan mutane, shi ma ana bashi wani abu a asusun shi. To don samun masu shiga su ga abin da ka dora, shi yasa komi ma sai kaga an dora a soshiyal midiya don waccan manufar. Yanzu ka lura, kusan duk hankalin mutane ya koma ga batun wadannan Aliens da ake magana, to duk wanda ya dora su, yawan mutanan da ya samu shi zai bashi damar kudi masu yawa, tunda yanzu an gano samun kudi ta wannan hanyar.
Matashin yace, babu ruwan mai aza irin wadannan labarai hatta da zagin da za'a yi mashi muddin dai za'ayi ta shiga a ga abin da ya dora. 

Post a Comment

Previous Post Next Post