Zaben2023 - ZABE YA GAJI A CI KO A FAÆŠI - Dokta Muhammad Sarki
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina.
Matashin É—an kasuwa kuma jagoran rukunin kamfanonin Al-Dusar Dokta Muhammadu Usman Sarki yayi nasiha mai ratsa jiki musamman ga 'yan siyasa masu takarar wasu kujeru tare da magoya bayan su. " Shi zabe ko na wane sashe ne dole wani yayi nasara wani kuma akasin hakan. Saboda haka nike amfani da wannan damar don taya murna ga waÉ—anda suka samu nasara tare da yin addu'ar Allah yayi masu jagora. Su kuma wadanda suka samu akasin hakan, ina rokon Allah ya musanya masu da mafi alkhairi.
"Don haka akai zuciya nesa a zauna lafiya a rungumi juna. Su kuma waÉ—anda Allah ya ba nasara muna masu addu'a Allah ya basu ikon sauke nauyin amanar da Allah ya É—ora masu ya kuma yi masu jagoranci suyi kyakkyawan shugabanci ga al'ummar da suke jagoranta", inji matashin É—an kasuwar Dokta Muhammadu.
Ya kuma kara da cewa, babban abin farin ciki a wannan zabe shi ne, irin yadda aka yi aka gama lafiya ba tare da samun tashin hankali ba kamar yadda wasu suka yi zato. "Kafin zaben, munji ana ta surutai iri-iri akan cewa za'a samu tashin hankulla, sai ga shi Allah cikin ikon Shi hakan bai samu ba kamar yadda aka yi zato. Sai dai wasu wuraren da aka nemi yin tashin hankalin amma dai mai iko da komi ya hana. Saboda haka, anan ma ina so inyi amfani da wannan dama in sake yin kira ga zabe mai zuwa, wato, na Gwamnoni da 'yan majalisun jihohi da ayi koyi da irin wanda aka yi na Shugaban kasa da 'yan majalisun wakillai na tarayya na jijircewa a fito ayi zaben kuma a kaucewa duk wani abin da zai kawo bacin rai balle har a samu damar yin fada. Karshe ina fatan ayi sauran zabukan masu zuwa lafiya,wanda hakan zai hana yin asarar dukiya da rayukan jama'a.