'YAN KASUWA 'YAN-UWAN JUNA SUN TAYA GWAMNA MASARI MURNAR CIN ZABEN TINUBU

'YAN KASUWA 'YAN-UWAN JUNA SUN TAYA GWAMNA MASARI MURNAR CIN ZABEN TINUBU

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 

Bayan baiyana sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayyar da aka gudanar a satin da ya gabata wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta shelanta nasarar cin zaben ga dan takarar jam'iyar APC Sanata Bola Ahmad Tinubu inda ya kayar da abokan karawarsa Atiku Abubakar na PDP tare da Peter Obi na LP inda shi Tinubun bayan samun kason da ake bukata daga jihohi, ya kuma basu tazara da yawan kuri'un da suka haurawa milyan biyu. 
Matasan 'yan kasuwar nan na Jahar Katsina wadanda kuma suke 'yan-uwan juna ne, wato, Alhaji Dahiru Usman Sarki shugaban kamfanin Danmarna Petroleum da kuma Dokta Muhammadu Usman Sarki shugaban rukunonin kamfanin Al-Dusar sun kaiwa Maigirma Gwamnan Jahar Katsina Rt. Aminu Bello Masari ziyarar taya shi murnar nasarar cin wannan zabe a matakin kasa da jam'iyar APC mai mulki ta samu.
Kamar yadda shi Alhaji Dahiru Usman Sarki ya shaidawa Gwamna Masari, wannan nasara ta Tinubu na daga cikin irin amsa addu'o'in da al'ummar kasa ke yi na Allah ya zabawa jama'ar kasa shugaba mafi alheri ga kasar, Allah kuma ya amsa. Ya kara da cewa, al'ummar Jahar Katsina da ma kasa baki daya na da yakin wannan sabuwar gwamanti mai zuwa zata yi bakin kokarinta na kawo karshen matsalolin da ake fuskanta musamman akan batun tattalin arziki da kuma tsaro, kamar yadda shi Gwamnan yake yi a cikin jahar wanda kuma ake ganin alfanun abin. 
Acikin dan gajeren jawabin da yayi, Alhaji Dahiru a madadin abokan tafiyar shi, sun zo ne don yiwa Gwamna murna da kuma addu'ar fatan alheri musamman ga shi Gwamnan a sauran rayuwarsa a nan gaba bayan ya bar kujerar mulki. "Ba zamu taba mantawa da irin fadi tashin da kayi ba na ganin ka kawowa jahar Katsina cigaba ta fuskoki da dama duk kuwa da tarnakin rashin tsaron da aka rika samu, hakan bai hana ka cinma nasarar kashi tamanin da biyar zuwa tis'is cikin dari acikin shekarun da akayi akan wannan kujera wadda tun farko ka amshe ta tattare da matsalolin tattalin arziki da kuma batun tsaron. Mu al'ummar Jahar Katsina shaida ne akan irin namijin kokarin da kayi. Muna fata wanda zai gaje ka ya aza harma ya wuce inda ka tsaya a wajen cigaban Jahar. 
A nashi jawabin Gwamna Aminu Bello Masari ya godewa wadannan matasan 'yan kasuwa tare da jinjina masu musamman ta irin yadda suka sabkewa gwamnati wasu nauye-nauye ta hanyar samawa musamman matasa aiyukan yi a kamfanonin su. Ya kuma yi jinjina tare da mika godiyar shi ga mahaifin 'yan kasuwar wato Alhaji Usman Sarki wanda Gwamnan yace, basu bar gida ba wajen kawowa al'ummar Jahar Katsina abubuwan cigaba. Babban misalin da Gwaman ya kawo wanda shi Alhaji Usman Sarki ya bayar don cigaban al'umma duniya da lahira shi ne, bude makarantun addini wanda ya hada su da na zamani. "Duk mutumin da koyar da kai addini domin ka san Allah don ka bauta mashi, sannan kuma ya koyar da kai yadda zaka samu ilmin zaman duniya domin samun hanyar dogaro da kai, ai wannan mutun baya ga addu'a babu abin da zaka yi mashi domin ya gama komai". 

Post a Comment

Previous Post Next Post