YADDA GIDAUNIYAR SDA KE TALLAFAWA MARASSA GALIHU A KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
An kafa Gidauniyar SDA don tallafawa marassa galihu ko gajiyayyu, daliban da basu iya biyan kudin makaranta, marayu, mata masu kananan sana'o'i da kuma matasan da ake koyawa sana'a domin dogaro da kai.
Shugaba kuma wanda ya kafa wannan gidauniya Alhaji Shamsuddeen Dahiru Ahmad ne ya shaidawa wakilin ASKGLOCNEWS cewa, yayi tunanin kafa waccan gidauniya domin lura da irin halin da al'umma suke ciki musamman wadanda aka lissafa, wadda gidauniyar ta wuce shekaru hudu da kafa ta. Kuma tun lokacin da aka kafa wannan gidauniya, "nine nike daukar nauyin aiwatar da komi na gidauniyar ba tare da na nemi gudunmuwa daga wani mutun, kungiya ko gwamnati ba. Ina amfani da abin da Allah ya hore mani daga cikin dan abin da nike samu.
Shugaban gidauniyar ya danyi tsokaci kadan daga cikin irin tallafin da wannan gidauniya ta bayar. "Akwai kwamiti mai kula da abin da ya shafi matsalolin dalibai wanda ke bayar da shawarar abin da ya kamata ayi, bayan sun yi bincike akan abin da dalibin ya kawo koke. Ta fuskar marayu, duk da cewa kowane lokaci ana tallafa masu, amma mun fi basu tallafin acikin watan azumi. Muna basu kayan masarufi tare kuma da É—unkin salla ta yadda zasu fito kamar masu iyaye. Kazalika, kwamitin dake aiwatar da wannan aiki na marayu muna sanya shi ya binciko wasu marayun wadanda suke fuskantar wasu matsaloli na daban. Misali, lokacin damina ko batun biyan kudin haya da sauran irin su".
A doguwar tattaunawar da muka yi da shi, Alhaji Shamsu yace, dukkan aiyukan da gidauniyar ke yi tana bin tsari ne kuma ta hanyar kwamitocin da aka kafa. Shugaban ya ce, hatta da makabartu wannan gidauniya bata barsu a baya ba. "Muna sayen tukane muna kaiwa tare kuma da fidda wasu lokutta don yin gyare-gyaren kaburran da suka samu lalacewa, wato, samun hujewa da sauran su. Wannan aiki na makabarta ba wai cikin garin Katsina kawai muke yin shi ba, a'a, akwai irin su Batagarawa, Rimi, Charanci da kuma Kurfi.
"Akwai ma wani lokaci da wata baiwar Allah taga wata yarinya a wajen Gadar Nayalli ta fitowa don yin bara. Gurguwa ce yarinyar, ita wannan mata jin labarin wannan gidauniya tayi taje ta shaidawa iyayen yarinyar. A takaice dai wannan gidauniya ta sayo keken guragu ta tallafawa wannan yarinyar", inji Alhaji Shamsuddeen Dahiru Ahmad shugaban gidauniyar SDA dake Katsina.