MUSULMI SU YI RIKO DA DARUSSAN DAKE CIKIN WATAN RAMADAN - Ɗanmajen Hausa

MUSULMI SU YI RIKO DA DARUSSAN DAKE CIKIN WATAN RAMADAN  Ɗanmajen Hausa
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
Ɗanruwatan Katsina, Ɗanmajen kasar Hausa, har ila yau, tsohon ɗan takarar Gwamnan Jahar Katsina a karkashin tutar APC wanda kuma a halin yanzu yake Mataimaki na musamman ga Gwamnan babban banki Najeriya CBN, Alhaji Abbas Umar Masanawa yayi kira ga jama'ar musulmi da su cigaba da yin riko da darussan da watan azumi na Ramadan yake koyarwa ba wai kawai sai a cikin watan ba. Alhaji Abbas yayi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilin ASKGLOC NEWS a Katsina. "Babban abin da azumi ke koyarwa shi ne, hakuri da juriya. Sannan yana kara kusantarmu ga mahaliccinmu. Kazalika, yana kara soyayya atsakanin mu musamman idan muka lura da wajen yin sallar jam'i da kuma wajen wa'azi. Mu lura anan babu mai shi da maras shi. Duk wuri guda muke haduwa. Kazalika, lokaci ne na taimakawa marassa karfi da mabukata. Saboda haka, yana da kyau wadannan abubuwa mu rike su mu cigaba da yi koda bayan azumin, domin mafi lokutta sai kaga da zarar lokacin ya wuce, shi ke nan kuma sai wata shekarar. Barin yin haka gaskiya ba karamar asara ba ce".
Ɗanmajen Hausar ya kara tunasarwa musulmi cewar, wata ne wanda Allah ke yiwa bayin shi gafara, ya 'yanta wasu daga azabar wuta. Sannan wata ne wanda Allah ke lunka ladar aikin alheri, har ila yau, ya nunka zunubi ga mai sabo. "Wata ne wanda ake samun shi sau daya acikin shekara amma falala da karamomin dake cikin shi suna da yawa. A cikin shi ne Allah ya fara saukarwa da Manzon tsira da Alkur'ani. Kamar yadda Allah ya fadi acikin sura Baƙara, aya ta 183-85. Sannan acikin shi ne kowa ke fatan ganin wannan dare wanda yafi sauran darare, wato, "Lailatul Ƙadri".
Sai dai Ɗanruwatan Alhaji Abbas Umar Masanawa ya nuna damuwar shi musamman akan irin yadda ake samun hauhawar farashin kaya acikin wannan wata, ba ma kamar irin na abinci ko abin sha wanda mai azumi zaiyi amfani da shi a lokacin buda baki. Akan haka,Alhaji Masanawa yayi kira ga 'yan kasuwar mu akan cewa, su ji tsoron Allah su sani duk abin da zasu samu acikin wannan wata ba zai yi masu komi ba. "Mu lura da makwabtanmu ta fuskar addini. Lokacin hidimar mu rage farashin kaya suke yi, to mu me ke dalilin tsauwalar da muke yi ga junan mu duk kuwa da wadancan ni'imomi da Allah yayi mana?", tambayar da Danruwatan kuma Ɗanmajen Hausa Alhaji Abbas Umar Masanawa yayi kenan.
Da ya juya akan zaben shugabannin da aka kammala a kwanan nan, yayi masu fatan alheri tare da yi masu addu'ar samun nasara a lokacin gudanar da mulkinsu. Sai dai ya tunasar da su akan batun jin tsoron Allah tare da yin mulki acikjn adalci. Sannan su sani, a matsayin su na shugabanni duk da ta hanyar jam'iya suka hau kujerun, to amma a wajen gudanar da mulkinsu babu maganar bambancin siyasar domin kowa ya zamo karkashin su. 

Post a Comment

Previous Post Next Post