Hajj 2023 - HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA TA SAKE TUNASAR DA MANIYATA AKAN KUDIN AJIYA

Hajj 2023 - HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA TA SAKE TUNASAR DA MANIYATA AKAN KUDIN AJIYA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
An sake tunasar da maniyatan aikin Hajji na 2023 akan batun kudin ajiya na mafi karanci na naira milyan biyu da rabi da su hanzarta kai wadannan kudade a ofishin hukumar mafi kusa da su ta hanyar kai takadar shaidar biya a banki. 
Kamar yadda wata sanarwar da ta fito daga ofishin Kakakin hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ta sanar maniyatan da suka fara ajiye kudin ajiyar su na naira milya guda da rabi da su hanzarta kai cikon naira milyan gudan don cike gurbin kamar yadda hukumar Aiyukan Hajj NAHCON ta kasa ta aiyana kafin sanin tahakikanin kudin aikin na bana. 
Alhaji Bello Karofi wanda yayi bayanin haka a madadin Babban Daraktan hukumar Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ya kara da cewa, "har yanzu tsarin wannan hukuma anan Jahar Katsina yana nan akan wanda ya fara biya shi za'a fara ba fifiko. Sannan muna Æ™ara kiran maniyatan da su hanzarta biya ko cika wadancan kudi ga wadanda suka fara ajiyar domin hakan zai Æ™ara ba wannan hukuma damar sani tare da cigaban shirye-shiryen aikin mai zuwa", inji Jami'in hulda da jama'a (PRO) na hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina Alhaji Badaru Bello Karofi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post