Hajj 2023 - HAR YANZU KOFAR AJIYAR KUƊIN AIKIN HAJJIN BANA BUƊE TAKE A JAHAR KATSINA

Hajj 2023 - HAR YANZU ƘOFAR AJIYAR KUƊIN AIKIN HAJJIN BANA BUƊE TAKE A JAHAR KATSINA 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 
Har yanzun Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar katsina na sanar da maniyatan aikin Hajjin 2023 cewar har yanzu hukumar na cigaba da karbar kudin ajiya na naira miliyan biyu da rabi(N2.5milyan)kazalika, hukumar na cigaba da yin rejistar wadanda suka zuba kudin ajiyar su ga hukumar kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi a madadin Babban Daraktan hukumar Jin dadin Alhazai na Jahar Alhaji Sulemain Nuhu Kuki, ya shaida. 
Sanarwar ta tunasar da wadanda suka fara bayar da ajiyar su ta naira milyan guda da rabi da suyi kokarin cika sauran naira milyan guda domin su kai adadin abinda hukumar Alhazai ta kasa ta bayar da umarnin fara ajiyewa kafin sanin yawan adadin kudin da za'a biya. Maniyatan zasu biya wadannan kudade a cibiyoyin hukumar jin dadin alhazan mafi kusa da su dake cikin Jahar ta hanyar shaidar takardar bankin da suka biya kudin. 
Hukumar na gab da fara taron bita ga maniyatan domin sanin makama tare da sanin yadda ake yin aikin Hajji. Har ila yau, hukumar na kara jan hankalin maniyatan da su guji yin mu'amulla da bata gari musamman a wajen yin canji ko cewar zasu kai masu kudin ga hukumar ko wani jami'in hukumar. Hukumar tana karbar takardar shaidar biyan kudin ne daga baki. 

Post a Comment

Previous Post Next Post