Da dumi dumi GWAMNA MASARI YA SAKEWA HUKUMAR SUFURI TA JAHAR KATSINA SABON SHUGABA

Da dumi dumi - GWAMNA MASARI YA SAKEWA HUKUMAR SUFURI TA JAHAR KATSINA SABON SHUGABA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 

Wata sanarwar da ta fito mai dauke da sa hannun Sakataren gwamnatin Jahar Alhaji Muntari Lawal ta ce, an sallami shugaban hukumar sufuri KTSTA Alhaji Bilyaminu Muhammad Rimi daga mukamin jagorancin hukumar nan take, sannan ta nada sabon shugaban da zai jagoranci hukumar.
Gwamnan Jahar ta Katsina Rt. Aminu Bello Masari ya amince da nada Alhaji Gambo Abdulkadir Rimi a matsayin wanda zai jagoranci hukumar. Kamar yadda sanarwar tayi nuni, shi dai Alhaji Gambo ba bako bane ta wannan fuska domin ya taba jagorancin ta a wani lokaci can baya. 

1 Comments

Previous Post Next Post