CI GABA DA MULKIN APC A JAHAR KATSINA ALHERI NE - Ibrahim Teacher
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Anyi kira ga al'ummar Jahar Katsina da cewa, su sake zaben jam'iyar APC domin ci gaba da aiyukan alherin da Gwamna Aminu Bello Masari yake cikin yi wanda ya zamo a zahiri ga al'umma ba badini ba. Daya daga cikin matasa kazalika, daya daga cikin mukarraibai kuma na hannun daman Gwamna Masari, har ila yau, Babban mataiamki na musamman akan harkokin cikin gida a gwamnatin ta Masari, kazalika, Basarake, wato, Alhaji Ibrahim Teacher Sardaunan Galadiman Katsina Hakimin Malunfashi ne yayi wannan kira a lokacin wata tattaunawa da wakilin ASKGLOC NEWS bayan sanarwar dage zaben da hukumar zabe mai zaman kanta tayi ya zuwa 18/3/2023.
"Ina so jama'ar Jahar Katsina su tuna cewar tun lokacin da gwamnatin APC ta fara mulki a Jahar ta kawo abubuwan cigaban al'umma. Bari in fara da abin da ake yawan magana akan shi, wato, batun tsaro. Jama'a sun manta da cewar wannan matsalar gadon ta muka yi? Ko mun manta da batun Boko Haram ne? Ana maganar kidinafin da sauran su. In bamu manta ba, Maigirma Gwamna Masari shi ne Gwamna na farko da ya fara yunkurin kawo karshen hare-haren 'yanbindigar nan tun ma suna yi don satar shanu. An samu sauki sosai a lokacin duk da rashin samun cikakken goyon bayan da ya samu daga wasu sassa. Bai gajiya ba, ya cigaba da wannan kokari don ganin al'ummar jahar Katsina sun zauna lafiya. Cikin wannan kokari in ba zamu manta ba har maƙwabciyar kasa ta Nijer ya je. Amma da yake abin akwai zagon kasa da ake yiwa mulkin, duk wani shiri da ya kawo sai da aka lalata shi. Har zuwa yanzu maganar da muke yi kai wannan batu bai bar shi ba na ganin jama'ar shi tana cikin amimci, kuma Alhamdulillahi komi na yin sauki ba kamar a baya ba".
Teacher ya kara da cewa, irin gudummuwar da gwamnatin APC ta bayar ga kungiyoyi babu wata gwamnatin da tayi haka a can baya. "Mu dauki misali akan cigaban matasa ta fuskar hana su zaman kashe wando. Allah ya horewa al'ummar jahar Katsina matasa masu fikira da fasaha. Gwamnatin APC ce karkashin Gwamna Masari ta bullo da wani shiri na zakulo masu irin wannan fikira a tsakanin matasan ta kuma yi ruwa da tsaki wajen karfafa masu guiwa. Hakan yasa ta bullo da gasa ta fuskoki iri-iri ba don komi ba sai don ganin cewar matasan nan sun samu abin yi. Abu ne wanda yake a fili. An ga irin kokarin da kuma makudan kudaden da aka kashe. Wani abin farin ciki, daga cikin irin wadannan matasa yau akwai wanda yake kasashen waje yana karo ilmi akan irin basirar da Allah ya ba shi. Gwamnatin APC ta kawo wannan ba kuma tare da nuna wani bambancin siyasa ba. Kai hatta da wadanda suka shiga gasar basu yi nasara ba sai da aka yi masu wani abu.
Maitaimakawa Gwamnan akan al'amurran cikin gida bai tsaya anan ba dangane da bayanin irin aiyukan alheri da kuma cigaban da gwamnatin APC karkashin Gwamna Masari ta ba, ya kara da cewa, har zuwa yau babu wani ma'aikacin jaha da zaice yana bin bashin kudin albashin shi. Inma har anga jinkiri a lokacin biyan albashin, to daga bankin da ma'aikacin ke yin ajiya ne. Haka wajen fansho. Batun giratuti kuma, jama'a shaida ne akan irin dimbin bashin da gwamatin APC ta taras amma kuma cikin ikon Allah sai da ya zo babu wanda ba'a biya shi ba ko ba'a biya magadan shi ba. Kuma har yanzu ana cigaba da biyan wadanda suka ajiye aikin bisa tsari.
"In ka mance bari in tuna maka. Shin ko kasan cewar gwamnatin APC ce mai ci a yanzu tunda ta hau mulki har zuwa yau duk wani maniyacin da yaje aikin Hajji sai Gwamna Masari ya bashi kudin Saudiya Riyal 300? Tunda ya hau har zuwa yau ba'a bari ba, kuma kaf din Najeriya jahar Katsina ce ke bayar da irin wadannan kudade karkashin mulkin APC. Kai in takaice maka, don kawo cigaba da kuma ba kowa dama da hakki, gwamnatin APC ce ta baiwa kowa damar shiga kafafen yada labarai na gwamnati musamman jam'iyun adawa domin shiga su fadi albarkacin bakin su sabanin abinda ta taras a baya. Su kansu jam'iyun shaida ne akan haka. In zan cigaba da lissafo maka Aiyuka da abubuwan cigaban da wannan gwamnati ta kawo muna iya kwana nan. Yanzu ka dubi fannin ilmi. Wai ana cewa, an kashe biyan kudin jarabawar kyauta da ake yi. Wa ya kashe kuma ina aka kashe? Ka auna yadda ake cin jarabawar a wancan lokaci da yanzu. Wancan lokacin ance an biyawa yaro jarabawa, amma kuma baya cin jarabawar, kenan me aka yi? Amma yanzu duk yaron da aka biyawa jarabawar kai ba sai an gaya maka ba, babu asarar aciki.
Da ya juya akan dsntakarar Gwamna Dokta Dikko Radda, Alhaji Ibrahim yace, "yo ai ana cewa, mai kamar zuwa kan aika. Kana tunanin inma ba samu lunki akan abinda Masari yayi ba sau goma kana zaton za'a samu akasi? Duk surutai ne na siyasa da ake cewa ya samu wani matsayi bai taimakawa jama'a ba. Irin wannan tsogumin kuma dole a rika samun shi ga É—an-adam. To don ni ban samu ba shike nan sai ace kowa ma haka ne? Ai su wadand suka ci gajiyar kuma suna cikin ci in baya ga godiya kaji suna wata magana. Saboda haka sake zaben jam'iyar APC wadda Dokta Dikko Radda ke yiwa takara cigaban alheri a Jahar Katsina. Ba sai na fito na maimaita manufofi da kudororin shi ba, kowa ya ji kuma mun gamsu. Iyaka kira zanyi ga al'ummar Jahar Katsina da su fito ranar 18 ga watan Maris na 2023 domin zabar É—antakarar mu kuma Gwamnan mu na gobe, Dokta Dikko Radda tare da Mataimakin shi Farouk Jobe da sauran 'yan takarar mu na majalisar jaha a karkashin jam'iyar mu ta APC mai albarka", inji Alhaji Ibrahim Teacher Babban Mataimaki na musamman akan harkokin cikin gida karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari.