Zaben Shugaban Ƙasa : MATASA ZASU ZAMO KAN GABA WAJEN ZABEN TINUBU - Hon. Kusada
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Tsohon Kakakin Majalisar dokokin na Jahar Katsina, Ɗan majalisar wakilai na Tarayya mai wakiltar karamar hukumar Kusada Honarabil Abubakar Yahaya Kusada ya ce, a zaben shugaban ƙasa da za'a yi nan da 'yan kwanaki masu zuwa, matasa ne zasu zamo kan gaba wajen zaben dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin tutar jam'iyar APC, wato, Sanata, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu domin haye wannan kujera.
Honarabil Kusada ya ce, "duba da irin yadda matasa maza da mata ke fitar farin ɗango don nuna goyon bayan a duk inda suka je yakin neman zabe a kasar nan, hakan ya nuna cewa, matasan na tare da ɗan takarar na su domin ganin cewa, ya hau wannan kujera. A hirar musamman da suka yi da wakilin ASKGLOC NEWS, Honarabil Abubakar ya ce, wannan mataki na nuna goyon baya da matasan suke wa Sanata Tinubu ba shi rasa nasaba da yakinin da suke da shi na cewa, zai kawo masu hanyoyin cigaba da kawar da zaman kashe wando ta hanyar kafa masana'antu da sauran su.
Da yake karin haske akan hasashen da wasu ke yi na ganin rashin cancantar dan takarar saboda yanayi na shekaru da kuma rashin lafiya, Honarabil Kusada ya ce, "kada jama'a su manta da cewa, ciwo da lafiya duk na Allah ne. Kuma tun daga lokacin da Tinubu ya fara yawon kamfen har zuwa yau, babu inda aka samu labarin cewa, ya gaza tashi ya yiwa jama'a bayani na sama da awa guda, balle ace ya samu wata lalurar da ta sanya shi ganin likita ko likita ya hana shi yawon. Kuma kowa yasan yadda yakin neman zabe yake ga dantakarar. Shin muna mantawa da cewar, yanzu ake haihuwar mutun kuma ya mutu nan take, wani ma babu ran za'a haiho shi? Sannan mutane nawa ke kwance a asibiti magashiyan amma kuma suna da rai masu cikakkiyar lafiyar ke mutuwa. Ko babu komi, mutuwar marigayi tsohon shugaban kasa Sani Abacha ta isa ta zamo izna gare mu. Kazalika, mu dubi marigayi shugaban kasar Zimbabwe Robert Morgabe. Wannan wani abu ne kawai na adawar siyasa.
Ɗan majalisar ya jinjinawa al'ummar Jahar Katsina musamman jama'ar da yake wakilta akan irin yadda suka fito wajen tarbar dantakarar shugaban kasar Sanata Asiwaju bisa ga yakin neman zaben da ya zo jahar Katsina. "Dole mu godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan irin yadda ya bar duk wasu hidimomin shi ya zo wajen wannan yakin neman zabe. Kazalika, ina so inyi amfani da wannan dama in mika sakon ta'aziyyarmu ga al'ummar kananan hukumomin Bakori da Kankara akan wannan iftila'in harin 'yanbindigar da yayi sanadiyar rasa rayukan wasu al'umma", inji Ɗan majalisar wakilai na Tarayya mai wakiltar karamar hukumar Kusada ta Jahar Katsina Honarabil Abubakar Yahaya Kusada.