ZABEN KUJERAR SHUGABAN KASA NAJERIYA DA YANMAJALISU MACE CE MAI CIKI
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
Zaben da ake cikin yi a Najeriya na kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun wakillai da dattawa a Najeriya har yanzu yana matsayin mace ce mai ciki.
Duk da wasu 'yan matsalolin da ake fuskanta a wasu wuraren musamman na zargin sayen kuri'ar masu jefawa hakan bai bada wani sahihin tabbacin ga jam' iyar dake kan gaba ba musamman a tsakanin APC da PDP bama kamar jihohin arewa maso yammacin kasar wadanda wasun su ke fama da matsalolin tsaro wanda hakan bai hana su fitowa don jefa kuri'ar su.
Kamar yadda wakilin ASKGLOC NEWS ya zagaya tare da tuntubar wasu sassan, 'yan takarar shugaban kasar su biyu, wato Atiku da Tinubu kowannesu na fatan ganin ya samu rinjaye a jihohin Katsina da Kano, sai Kaduna da Jigawa. Alabashi su jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi su zamo cikon gibin da ya rage. Amma har zuwa wannan lokacin babu wani sahihin tabbacin ga alamu ga wadda ke da rinjaye.
Wani abin lurar anan shi ne, irin yadda jama'a basu fito kamar yadda aka yi zabukan 2015 da 2019 ba. Wasu na cewa, saboda rashin kudi ne yayin da wasu ke cewa gajiya suka yi domin ba'a basu abin da suka zaba.
Ita dai hukumar zaben mai zaman kanta ta alwashin cewar maganar aringizon zabe ya kare, yayin da a hannu guda Shugaba Buhari ya sha alwashin duk wanda ya ci shi zai ba mulki babu wani kokonto ko jayayya