Zaben 2023 RUKUNONIN KAMFANIN AL-DUSAR SUNYI KIRA DA ABI DOKA A LOKUTTAN ZABE

Zaben 2023 RUKUNONIN KAMFANIN AL-DUSAR SUN YI KIRA DA ABI DOKA A LOKUTTAN ZABE
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 
Anyi kira ga al'ummar Najeriya da su bi dokoki a lokacin da kasar ke ta shirye-shiryen zabubbukan shekarar 2023. 
Rukunin kamfanonin AL-DUSAR karkashin shugabancin Dokta Muhammad Usman Sarki ne suka yi wannan kira ga É—aukacin al'ummar  Najeriya da cewa a guji kawo duk wani abu da zai kawo ruÉ—ani ga zaÉ“en na shekarar 2023 wanda ake sa ran farawa a ranar 25 ga watan Fabarairu a matakin zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisu na sassa biyu a matakin kasa dake cikin wadanda za'ayi zaben su a wannan rana. 
Kamar ya shugaban ya baiyana a tsangayar shi ta kafar sadarwar "Facebook", Dokta Sarki ya ce, "Sanin Kowa ne cewa, Najeriya na cikin halin da take buƙatar shuwagabanni na gari da zasu kawo cigaba mai amfani ga al'ummar mu,wanda har ma zai iya anfanar da wasu kasashen kasancewar Najeriya uwa ce ga kasashen Afirka"
"Saboda haka, akwai buÆ™atar yin hangen nesa da sanya natsuwa akan irin shuwagabannin da zamu zaÉ“a su jagorance mu a kowane mataki. Mu guji tada hayaniya a lokacin zaÉ“e ! Mu kasance masu bin doka da oda!  Mu guji duk wani abin da ka iya kawo asarar rayuka ko dukiyoyin jama'a a lokacin zabe! Idan muka kiyaye wadannan abubuwa a wannan lokaci mai muhimmanci, zamu samu nasarori tare da cigaba mai dorewa, hakan kuma zai kara kawo mana hadin kai da kishin kasarmu wadda bamu da wadda ta fita".
Dokta Muhammadu ya kara tunasarwa da  'yan kasa da cewa, ba sai da tashin hankali ko yin amfani da makami ake zaÉ“en Shuwagabanni ba, Æ™uri'ar ka yan'chinka kuma ita makamin da zaka yi amfani da shi don kawar da wanda kake ganin bai dace da ya jagorance ka ba, sannan kuma ita ce makamin da zaka yi amfani da ita don zabo shugaban da kake ganin zaiyi maka adalci tare da kawo mana hanyoyin bunkasa tattalin arzikin mu, kiwon lafiya,ilmi sannan da babban batu wato, sha'anin tsaro. Shugaban yayi addu'o'i na musamman ga al'ummar kasa baki daya da kuma fatan ayi wannan zabe a gama lafiya tare da fatan Allah ya zaba mana shugabanni na gari tun daga matakin kasa har zuwa ga jihohi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post