NSCDC DA IPMAN SUN HADA GUIWA DON KAWO KARSHEN KARANCIN MAN FETUR A JIHAR

NSCDC DA IPMAN SUN HADA GUIWA DON KAWO KARSHEN KARANCIN MAN FETUR A JIHAR KATSINA.
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
 Sabon kwamandan rundunar tsaro ta farin kaya da aka fi sani da "Civil Defence" a jihar, Kwamandan Jamilu Abdu Indabawa yace, hukumar shi zata kawo Æ™arshen matsalar karancin man fetur ta hanyar hadin gwiwa da kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN a jihar Katsina.
       
 Kwamandan ya baiyana haka ne a yayin wata ganawa da shugabannin kungiyar, a ranar 30 ga watan Janairu,2023. 
 Kwamanda Indabawa ya sake jaddada kudirin hukumar na magance karancin man fetur da ya haifar da dimbin al’amurran da suka yi illa ga samar da man fetur a Jahar Katsina. Ya bayyana cewa karkatar da man fetur da aka warewa jihar;  zagon kasa ne sannan rashin wadataccen wanda ake fitarwa ga kasashen waje yana kawo cikas ga kokarin gwamnati a matakin tarayya da jiha na ganin an samar da isasshen man. 

 Kwamandan ya gargadi ’yan kasuwar da kakkausan harshe, cewa an tura shi jihar Katsina tare da Æ™ara mashi kwarin guiwa don magance wannan matsala a matsayin wani bangare na aiyukan hukumar.  Ya kuma nuna rashin jin dadinsa da irin wahalhalun da karancin man fetur ke haifarwa ga talakawan Najeriya da ke bata sa'o'i masu yawa wajen yin layin man fetur.  Kwamandan ya kuma gargadi 'yan Kasuwa game da tara ko sayar da man ga ‘yan kasuwar bayan fage wadanda ka iya yin safarar sa zuwa kasashe makwabta.

 A karshe Kwamanda Indabawa, ya sake nanata manufar Babban Kwamandan na kasa Ahmed Abubakar Audi PhD, mni, OFR akan burinsa na gurgunta ayyukan masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da masu aikata laifuka ta hanyar tabbatar da sa ido, sintiri da sa ido kan samar da kayayyaki, rabon man fetur, tare da tawagar sashen dake yaki da masu barnata kayan gwamnati na rundunar da ke fafatawa da wadannan masu zagon kasa, da kuma tabbatar da an kare muhimman kadarorin kasa da kayayyakin more rayuwa a fadin jihar Najeriya baki daya.

 Shugaban kungiyar IPMAN karkashin jagorancin Alhaji Abbas Hamza ya bada tabbacin ba kwamandan goyon baya a shirye shiryen da suke yi domin ganin an ci gaba da samar da man da ake rabawa kuma ake sayarwa a jihar.  Sun kuma tabbatar masa da cewa kungiyar na yin iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance matsalar karkatar da man ta barauniyar hanya da wasu marasa kishin kasa ke aikatawa.  Hakazalika kungiyar ta ci gaba da cewa har yanzu suna aiki da umarnin gwamnatin jihar Katsina na hana sayar da man fetur ga ‘yan kasuwar bayan fage don hana fasa-kwauri ko sayar da kayan ga ‘yan fashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post