"MASARI FIM MAKERS" SUN KARRAMA SAKATAREN GWAMNATIN JAHA KATSINA

"MASARI FIM MAKERS" SUN KARRAMA SAKATAREN GWAMNATIN JAHA KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
  
   Darakta Aminu K-Eza shugaban Masari Fim Makers na mikawa Sakataren gwamnatin Jahar Alhaji Muntari Lawal Satifiket na karramawa a ofishin shi. 

Kungiyar masu shirya fina-finai ta Masari dake Jahar Katsina ta karrama Sakataren gwamnatin Jahar Alhaji Muntari Lawal bisa ga namijin kokarin da yake yi na tallafawa kungiyar don cigaban sana'ar su. Kamar yadda shugaban kungiyar wanda kuma yake Darakta ne a shirya fina-finan, Alhaji Aminu Mannir K-Eza yace a lokacin da 'yan kungiyar suka ziyarci ofishin Sakataren a gidan gwamnatin Jahar don girmamawa tare da karrama sakataren ta hanyar ba shi takardar sheda, "wannan Æ™ungiya na alfahari da kai ta kowace fuska. Irin gudummuwar da ka bamu musamman ta yi mana jagoranci har gwamnatin jaha karkashin jagorancin Mai girma Gwamna Masari ta dauki nauyin horas da masu wannan sana'a ta fim a cikin jahar har mutun 86 wannan ba karamin cigaba bane a gare mu. Wani abu ne wanda muke fita waje don koyo amma yau sai ga shi acikin gida, ko ma ince har cikin daki wanda kuma ta hanyar ka muka samu wannan dama. Wani abin ban sha'awa kuma shi ne, ba wai kawai abin ya tsaya ga horaswa ba ne, a'a, su kan su wadanda aka horas sai da aka bi su da kudin abin hawa, bayan kyaututtukan na'ura mai kwakwalwa ta hannu(Laptop) da aka baiwa wasu da suka yi kokari a wajen wannan horaswa. Kazalika, ina so in shaidawa Mai girma Sakatare cewar, hatta da malam da zo don bayar da wannan horo na tsawon kwanaki uku, sun ce, wannan shi ne karon farko da suyi wanna horaswa acikin jin dadi da kuma fahimta. Jagoran bayar da ilmi wanda kuma kwararre ne a wajen harkar fim, Darakta Mika'ilu Bin Hassan wanda aka fi sani da sunan Gidigo yace, anyi musayar ilmi ne a tsakanin juna ba wai sun koyar ba, domin irin yadda yaga mutanen da ke karbar wannan horo sun mayar da hankali kuma sun nuna sun san abinda suke yi. Har ila yau, malamin yace, a iya sanin shi, wannan shine karon farko da yaga wata gwamnati ta dauki nauyin horas da masu wannan sana'a kuma har mutun 86 a lokaci guda. Inda ana samunngwamnatocinmu suna yin haka, tuni da arewa ta cigaba ta fuskar wannan sana'a". 
  
A nashi jawabin Sakataren Gwamnatin Jahar Alhaji Muntari Lawal yace, shi kan shi ba shine wanda za'a yiwa wannan godiya, godiyar ta Maigirma Gwamna Masari ce, domin shine wanda ya bayar da kudaden da aka gudanar da wannan horo. Sai dai duk da haka, Alhaji Muntarin ya nuna farin cikin shi akan yadda aka fara kuma aka gama wannan horaswa lafiya kuma cikin nasara. Saidai ya ja hankalin 'yan kungiyar akan cewa, su sani harkar fim sana'a ce mai karfi ba kamar yadda wasu ke daukarta ba da cewa, ko shiririta ko wani abu makamancin haka. "Duk yadda kuka dauki wannan harka haka zata kasance maku. In an dauka da muhimmanci a ci ribar ta, in kuma mutun yayi mata rikon sakainar kashi, shi ya sani. Amma ina baku shawara akan cewa, kada kuyi wasa da wannan sana'a musamman da wannan karin ilmi da kuka samu wanda na tabbata an anfana". Alhaji Muntari ya shaida masu cewar zai isar da sakon godiyar ga Maigirma Gwamna Masari.
Shi dai wannan taron horaswa anyi shi ne akan abubuwa uku, yadda ake rubuta labarin fim, yadda ake daukar hoton fim da kuma yadda ake tacewar hotunan fim bayan an dauka domin a samu abin da ake so. An dauki tsawon kwanaki uku wajen gudanar da wannan horo karkashin jagorancin Mika'ilu Gidigo

Post a Comment

Previous Post Next Post