MAGAJIN GARIN KATSINA YA ZAMA SHUGABAN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI

MAGAJIN GARIN KATSINA YA ZAMA SHUGABAN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

 

Magajin Garin Katsina Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir 
Gwamna Masari ya nada sabon shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina. Magajin Garin Katsina Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir shi ne wanda ya zama sabon Shugaban hukumar jin dadin Alhazai inda ya maye gurbin tsohon shugaban Alhaji Yusuf Barmo wanda Gwamna Masari ya sallama daga wannan mukami.
Nadin Magajin garin ya zo bayan kwana guda da sallamar tsohon shugaban wanda har zuwa yau babu wani bayani daga gwamnatin na dalilin cire Yusuf Barmon. Sai dai wasu na hasaahen cirewar kamar tana da nasaba da batun siyasa musamman akan zaben da aka yi na shugaban kasa da wakillan majalisun kasar da ya gabata aranar Asabar 25 ga watan Fabarairu na 2023 

Post a Comment

Previous Post Next Post