KANWAN KATSINA YA ZAMA AMBASADAN ZAMAN LAFIYA NA FARKO DAGA CIKIN HAKIMAI
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Kanwan Katsina Hakimin Ketare Alhaji Usman Bello Kankara mni ya zama hakimi na farko a masarautar Katsina da ya samu lambar zama Ambasadan zaman lafiya da hukumar Hana fasa kwabri da aka fi sani da Kwastan ta bashi. Kanwan na Katsina wanda yake tsohon jami'an hukumar ne da ya ajiye aiki bayan share shekaru 35,ya samu wannan lambar gurmamawar ta zama Ambasadan zaman lafiya da hukumar Kwastan din ta kasa shiyar Katsina ta ba shi.
Kamar yadda aka baiyana a wajen ba shi wannan lambar girmamawa, hukumar tayi la'akari akan irin rawar da ya taka kuma yake cikin takawa hukumar musamman sake maido da kungiyar tuntuba ta masu ruwa da tsaki don ci gaba da wayar da kan al'umma a aiyukan hukumar musamman mazauna kan iyakokin jahar. Wannan aiki da yayi, ya sake farfado da kima da martabar hukumar da aiyukan ta a tsakanin al'umma. Kazalika, Alhaji Usman Bello ya aiwatar da tarin aiyuka na ci gaban al'umma ba wai ga masarautar shi, yanki, ko jaha ba hatta da kasa baki daya. In za'a iya tunawa, a lokacin da yake aiki, shi ne jami'i na farko da ya fara samawa hukumar hanyar samun kudin shiga musamman akan fiton busasshen kifi da ake yi a yankin tafkin Chadi, aikin da har yanzu ake amfana da shi.
Har'ila yau, baya ga samawa matasa abin yi, Kanwan Katsina ya janyo aiyukan wasu hukumomin kusa ga al'ummar shi, misali, hukumar kidaya, katin zama dan kasa da sauran su. Alhaji Usman Bello bai tsaya anan ba, domin ya kawo hanyoyo da dabarun samar da zaman lafiya da tsaro a yankin shi.
Da suke yabawa wannan karamci da hukumar Kwastan din tayi, Shugaban kungiyar 'yan jaridu ta kasa reshen Jahar Katsina Alhaji Tukur Hassan Dan'Ali tare da takwaransa na kungiyar marubatan labarin wasanni Alhaji Nasir Sani Gide, sun ce, Kamwan na Katsina ya cancanci samun wannan lamba ta la'akari da irin yadda yake huddodin shi da kungiyoyi da sauran jama'a. Mutun ne wanda yake jajircewa tare da yin tsayin daka na a duk lokacin da ya tunkari neman wani abin da yasan zai amfanar da jama'a don tattabar da samun abin. Kazalika, sun yabawa ita wannan hukuma da tayi nazari bayan kyakkyawan binciken da tayi har ta bayar da wannan muhimmiyar lambar girmama ta Ambasadan zaman lafiya ga shi Kanwan na Katsina Hakimin Ƙetare Alhaji Usman Bello Kankara