JAM'IYAR APC ZATA LASHE ZABUKAN 2023 - Garkuwan Kaita

JAM'IYAR APC ZATA LASHE ZABUKAN 2023 - Garkuwan Kaita

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 

An baiyana cewar jam'iyar APC ce zata lashe zabukan 2023 wanda ya kama tun daga na Shugaban Æ™asa har ya zuwa na 'yan majalisun jihohi. 
Shugaban matasan jam' iyar APC na Katsina ta tsakiya Alhaji Isma'ila Usman 'Yanɗaki Garkuwan Kaita kuma Magayakin 'Yanɗaki ya shaidawa manema labarai haka a garin 'Yanɗaki a lokacin da yaje jefa ƙuri'ar shi a zaben kujerar shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar asubuci 25 ga watan Fabarairu na 2023.
Shugaban matasan wanda ya nuna gamsuwa akan yadda aka kawo kayan zabe a cikin lokaci a dukkan rumfunan yanki shi da ma wasu sassan na Æ™aramar hukumar Kaita ya Æ™ara da cewa, "kamar yadda aka sani, mu a garin 'YanÉ—aki da Æ™aramar hukumar Kaita baki É—aya an san mutane ne masu son zaman lafiya. Akan haka ne yasa kuke ganin ana yin zaben acikin kwanciyar hankali a dukkan wuraren da ake yin zaÉ“en". 
Garkuwan Kaitan har ila yau, ya yaba da irin yadda matasa suka fito don kaɗa kuri'un su musamman na jam'iyar APC wanda hakan ya nuna alamun nasarar cinye sauran zabubbukan dake tafe. Alhaji Isma'ila yace, "ganin irin aiyukan alherin da jam'iyar ta shimfida tun daga matakin ƙaramar hukuma har zuwa ga ƙasa baki ɗaya yasa jama'a suke sake zaben jam'iyar." Mu dubi irin yadda aka shimfiɗa mana kwalta wadda in ka taso tun daga cikin garin Katsina zaka wuce har Ɗankaba zuwa Dankama ta wannan sashe na garin 'Yanɗaki, wanda hakan ya taimakawa jama'ar mu saukin tafiye-tafiye musamman ta fuskar kasuwanci domin mafi yawan jama'ar wannan yanki manoma ne da kasuwanci"
A Æ™arshe shugaban matasan ya Æ™ara yin kira ga jama'ar wannan jaha da kada su yi Æ™asa a guiwa a wajen zaben Gwamna da 'yanmajalisun jaha su sake zaben 'yan takarar jam'iyar ta APC. 

Post a Comment

Previous Post Next Post