Da dumi dumi - ƘUNGIYAR DILLALAN MAN FETUR TA JANYE UMARNIN DA TA BAYAR NA RUFE GIDAJEN MAI

ƘUNGIYAR DILLALAN MAN FETUR TA JANYE UMARNIN DA TA BAYAR NA RUFE GIDAJEN MAI
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta janye umarnin da ta bayar na rufe gidajen man fetur a fadin kasa baki daya. 
Wata sanarwa da ta fito mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kawa Alhaji Mohammed Kuluwa ta ce ta janye wannan umarni ne domin cigaba da tattaunawar da take yi da hukumomin da abin ya shafa. 
Tun farko dai sai da kungiyar ta umarci dukkan gidajen man fetur dake kasar da su rufe gidajen man har sai abinda hali yayi bisa zargin cewa, suna tafka asara. 

Post a Comment

Previous Post Next Post