Da dumi dumi - GWAMNA MASARI YA KORI WASU MUKARRABAN GWAMNATI

Da dumi dumi - GWAMNA MASARI YA KORI WASU MUKARRABAN GWAMNATI

 Daga Ahmed Kabir S/Kuka.
 
Kwana biyu rak da kammala zabubbukan kujerun shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya sai ga wata takardar sanarwa ta fi a ranar litinin din mai dauke da sa hannun Sakataren gwamnatin Jahar Katsina Alhaji Muntari Lawal inda ta sanar da cewa, Gwamna Masari ya soke mukaman wasu mutane 4 daga gwamnatin shi. Mutanen da Gwamna ya soke mukaman su nan take sun hada da Kwamishinan Aiyuka gidaje da sufuri Alhaji Tasi'u Dahiru Dandagoro da Alhaji Yusuf Barmo shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar jin dadin Alhazai da Fatima Ahmed Babbar Sakatariya a sashen Shirin cigaban maradun karni sai kuma Dokta Aminu Waziri Babban Sakatare a ma'aikatar gona. An kuma umarce su da su bayar da ragamar mulki ga na kusa ga kujerun su.
Duk da cewa, gwamnatin bata fito fili ta baiyana dalilan sokewar ba, amma wasu na hasashen cewa hakan baya rasa nasaba da batun zaben da ya gabata. 

1 Comments

  1. Haba Masari Hakuri ka Ya CUCI Jihar Katsina. Ai Tuntuni Yakama ace ka Binciki Maaikatar AYYUKA..

    ReplyDelete
Previous Post Next Post