AN KADDAMAR DA MEMBOBIN KWAMITIN GUDANARWA NA HUKUMAR SHARI'AR MUSULUNCI NA JAHAR KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ranar alhamis 9 ga watan Fabarairu na 2023 aka kaddamar da membobin kwamitin gudanarwa na hukumar Shari'ar musulunci a Jahar Katsina, wanda aka gudanar da bikin kaddamarwa a Babbar Kotun ÆŠaukaka karar Addinin musulunci dake cikin garin Katsina.
Alkalin Alkalai na Jahar Katsina Dokta Muhammad Kabir Abubakar
Kamar yadda Babban Alkalin alkalai na Jahar Katsina Dokta Muhammad Kabir Abubakar ya ce, kwamitin yana dauke da membobi 10 wanda a yanzu aka kara mutane 3 suka zama su 13 kamar yadda doka ta bada.
Kazalika, Alkalin alkalan yace, su mutane 10 na farko an sake barin su acikin kwamitin yayin da aka samu karin, Dokta Bishir Abdullahi malami daga jami’ar Umaru Musa 'Yar'adua, Malam Abdurrahman Jibrin daga Funtu'a tare da Malam Ibrahim Sabi'u Jibia.
Babban aikin wannan kwamiti dai shine, bayar da shawara ko kawo wasu gyare-gyaren da suka ga ya dace. Kazalika, wakillan suna zama su tattauna don kawo wasu abubuwan da suke gani zai kawo cigaba a ita hukumar shari'a.
A jawabin da yayi mai tsawo a wajen wannan kaddamarwa, Babban Jojin Jahar Katsina Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar yace hakkin wannan hukuma ne taga an sake farfado ko kuma an cigaba da aiwatar da wasu dokokin da suke ba baƙi bane ba a shari'ar musulunci sai dai kawai rashin yin aiki da su. Misali, kare hakkin mata da kananan yara, yawan sakin aure barkatai da sauran irin su, wadanda duk addinin musulunci ya tanade su. Ya kara da cewa, duk wata doka ko kare wata doka a duniya, shari'ar musulunci ta zo da shi. Ya kawo misali da cewa, dokar musulunci ta kare hakkin yaro tun kafin ya zo duniya ta hanyar samar ma shi da iyaye na gari, suna na gari, ilmi dq sauran su. Dokar da ta wajabtawa 'ya'ya daukar nauyin iyayen su saɓanin wadda ake kai iyayen gidan gajiyayyu ko tsaffi su kuma yaran su dawo su cigaba harkokin su ba tare da sun kara kulawa da su ba wai saboda ci gaba. Dokar da ta tanadi bayar da gado ga magada idan an mutu, sabanin barin wasiyyar a baiwa Kare ko Mage dukiyar idan an mutu, bayan ga 'ya'ya ko magada da rai. Amma abin takaici, wai har sai azo ace, wannan doka za'a yiwa gyara ko kuma ba'a ma san da ita ba. Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar ya ja hankali sosai akan yadda shari'ar musulunci take, wadda har yayi nuni cewa, aikin wannan kwamiti ne da ya samo wata hanyar ilmantar da jama'a musamman akan yadda ake amfani da waɗannan kafofin sadarwa na zamani.
A na shi Jawabin, Gwamnan Jahar Katsina wanda ya samu wakilcin Kwamishinar Shari'a Barista Asma'u, tace, Gwamnan ya nuna damuwar rashin halartar shi a wurin saboda wasu lalurori,sannan kuma ga shi wannan shine wa'adin mulkin shi na karshe. Akan haka yayi kira ga su wadannan membobi da su yi aikin su tsakani da Allah, sannan su sani gwamnati zata cigaba da basu goyon baya tare da basu duk wani hadin kai domin ganin sun sabke nauyin da ya rataya kansu.
Shi ma Shaihin Malamin nan Sheikh Yakubu Musa Hassan wanda yayi jawabi a madadin sauran 'yan kwamitin bayan yayi godiya ga Allah, ya jaddada cewa, da ikon Allah zasu yi iya kokarin su na ganin sun sabke wannan nauyi wanda zasu yi tsawon shekaru 4 nan gaba suna dauka.