ƘUNGIYAR WASAN POLO TA KATSINA TA SAMU SABBIN SHUGABANNI

ƘUNGIYAR WASAN POLO TA KATSINA TA SAMU SABBIN SHUGABANNI

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

Ƙungiyar wasan Polo(Katsina Polo Club) ta sami sabbin Shugabanni domin tafiyar da harkokin ƙungiyar waɗanda ke tafiya daidai da zamani. Samar da sabbin shugabannin ya biyo bayan aje muƙamai don ƙashin kai da shugabannin baya suka yi. Kujerun Babban Shugaba(President) Shugaba(Chairman) da kuma Sakataren ƙungiyar suka yi a kwanakin baya. 
  
Ajiye muƙaman waɗancan shugabannin yasa membobin ƙungiyar suka yi saurin naɗa kwamitin gaugawa domin riƙe harkokin ƙungiyar har zuwa ranar wannan lahadi 8 ga watan Janairu 2023 domin tabbatar da shugabannin da zasu riƙe ƙungiyar. 
A ranar 3 ga watan Janairu 2023 Maimartaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmuminu Kabir ya tabbatarwa da Alhaji Sanusi Kabir(Karshin Katsina) da matsayin Babban Shugaba(President) na wannan ƙungiya. Kazalika, a ranar lahadin a wajen taron da membobin ƙungiyar suka yi suka tabbatarwa sauran waɗanda aka zaɓa a matsayin riko a baya da cewa, yanzu an amince da su cigaba da riƙe muƙaman da suke a kai ta hanyar amincewar membobin. Kazslika, za'a cike sauran gurabun da babu su a ƙungiyar domin samun damar aiwatar da harkokin ƙungiyar a bisa doka da oda. 
A lokacin da ya yiwa membobin ƙungiyar jawabi, Babban Shugaban Alhaji Sanusi Kabir ya ja hankakin membobin akan batun haɗin kai domin shine babban abinda ake bukata. Sannan zasu yi iyakar ƙoƙarin su na ganin cewa, suna da tarihin da ƙungiyar take da shi akan batun wasan na Polo yana nan daram sai ma abin da zai cigaba.
Shugabannin da aka amince da su cigaba da riƙe muƙaman na su, sun haɗa da Alhaji Muhammadu Usman Sarki a matsayin Shugaba, Alhaji Ibrahim Daku a matsayin Sakatare, Dotka Aminu Waziri Mataimaki na ɗaya, da Alhaji Madani Sani a matsayin Mataimakin shugaba na biyu. Kujerar da aka baiwa marigyai Alhaji Bishir Mangal an baiwa Alhaji Lawal Dshiru Mangal ta ɗaya daga cikin shugabannin da zasu jagoranci ƙungiya(Ex-officio). Malam Umar Kabir zai cigaba da riƙe mukamin Kodinato da sauran wasu muƙaman. 
Kazalika, za'a sake sabunta rejistar membobin ƙungiyar tare da sabunta katin shedar zama ɗan ƙungiyar. An daiyi taron a ɗakin taro na Aldussar Zoo and Park. 

Post a Comment

Previous Post Next Post