Tsaro:...ZAN ƘWATO DUK WANI DAJIN DA AKA SAYAR A JAHAR KATSINA - Sanata Ɗanmarke

Tsaro: ZAN ƘWATO DUK WANI DAJIN DA AKA SAYAR A JAHAR KATSINA - Sanata Ɗanmarke

Daga Kabir Ahmed S/Kuka

Dantakarar kujerar Gwamnan Jahar Katsina ƙarƙashin jam'iyar PDP Sanata Garba Yakubu Lado Ɗanmarke yayi alƙawalin daukar wasu matakai domin maido da Jahar cikin hayyacinta muddin aka zaɓe shi ya zama Gwamna. 

 Ɗantakarar ya baiyana haka ne a wajen taron zauren al'umma wanda kamfanin buga jaridun Aminiya, "Dailytrust, Trust Radio/TV" tare da cibiyar Demokaradiya da cigaban al'umma tare da kamfanin jaridar Yanar gizo ta "KatsinaCity News" suka gabatar a ranar Asabar 14 ga watan Janairu na 2023.
Daga cikin abubuwan da Sanatan ya ce zaiyi in an zabe shi, sun hada da babbar matsalar dake ciwa al'ummar tuwo a ƙwarya, wato, batun tsaro. Ya nuna takaicin shi akan irin yadda ake tafiyar Hawainiya akan batun. Akan haka, ɗan takarar yace, daga cikin matakan da zai dauka don shawo kan matsalar har da batun ƙwato dazuzzukan da yace duk an sayar da su. Sanatan ya ƙara cewa, ta yaya fulanin nan zasu rayu bayan an san cewa basu da inda suke rayuwa da dabbobin su irin cikin dajin. Yau an wayi gari duk an sayar da dajin, dole kuwa a samu matsala. Don haka, yana da kudurin kwato duk wani dajin da aka sayar domin mayar da shi bisa muhallin shi don hakan zai taimaka wajen kawo karshen waɗannan aiyukan ta'addanci.
Dantakarar kujerar Gwamnan da ya juya akan batun matsalar shaye-shaye wadda mafi yawa ake aza samun wasu matsalolin ta wannan hanyar. Sanatan ya ce, babban abin da zai fara yi a wannan fannin shi ne, yaƙi da matsalar daga manyan ma'aikatan gwamnati dake da wannan mu'amulla. "Babu yadda za'ayi mai aiwatar da abu kuma azo ace wai zai hana aiwatarwa. Saboda haka, zan dauki mataki daga manyan dake tu'ammali da waɗannan shaye-shaye. Yin hakan zai kawo karshen da na baya zasu koyi darasi. Har'ila yau, dantakarar yace, zaiyi amfani da kwarewarshi ta fuskar kasuwanci domin gaiyato kamfanoni daga waje don farfado da tattalin arzikin Jahar. Sannan za'a bullo da hanyoyin samarwa matasa aiyukan yi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post