TARON KADDAMAR DA TAKARAR YAKUBU LADO NA PDP YA GIRGIZA WASU A JAHAR KATSINA - Al'umma
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Taron kaddamar da ɗantakar kujerar Gwamnan Jahar Katsina a ƙarƙashin jam'iyar PDP wanda Sanata Yakubu Ɗanmarke/Aminu 'Yar'aduwa ke yi wanda aka yi a filin Aya dake cikin garin Funtua a ranar Larabar da ta gabata ya zowa da jama'ar Jahar ɗan bazata ganin irin yadda wasu ke ganin kamar jam'iyar adawa ta nufi fagen durƙushewa bisa ga ricikin cikin gida. Kamar yadda muka zagaya don jin ta bakunan jama'a akan irin yadda wannan taron ƙaddamar da shi ɗan takarar ya gudana, mafi rinjayen waɗanda muka zanta da su sun nuna mamkin irin yadda ɗinbin jama'a suka taru don nuna goyon bayan su ga ɗantakarar.
"Wannan taron gaskiya ya nuna a fili cewar, da ikon Allah jam'iyar PDP zata sake kafa gwamnati a Jahar Katsina. Inbaccin taron Atiku dake neman shugabancin ƙasa da yayi anan Katsina wanda za'a ce wasu daga wasu jihohin sun zo, gaskiya ace ɗan takarar gwamna ne ya tara waɗannan jama'a kuma daga jam'iyar adawa ba mai ci ba, wannan ya nuna a fili alamun samun nasara gare mu",inji Malam Musa. Shi ma Haruna Daga cewa yayi, "lokacin da muke kan hanyar zuwa garin na Funtua, zuciya ta bugawa take saboda ban san irin yadda zamu samu kanmu ba. Amma tun daga wajen Bakori na fara samun natsuwa ganin irin yadda mutane ke tafiya zuwa garin na Funtua. In takaita maka, motar mu nan baya muka ajiye ta muka hau babura zuwa filin taron. Ai yadda na gani, farko sai nayi zaton kamar ranar Arfat ce irin yadda naga taron jama'a kuma kowa cikin farin ciki. Gaskiya taron yayi mani ɗan baka zata ba".
Duk da cewa, yankin na Funtua na daga cikin yankunan da ake fama da matsalar tsaro, hakan bai sa jama'a sun karaya zuwa taron ba kuma acikin sakin jiki da walwala. Wannan baiwar Allah da tace kada a fadi sunanta tace, "matsayina mace wadda ke da rauni kuma aka ƙara mani wani raunin ta hanyar bari na da marayu, wallahi ko ina ne wannan jam'iya zata yi sai naje domin ba zan manta baya. Tabbas ina da yakinin za'a sake samun zaman lafiya muddin PDP ta ci wannan zaben. Tattalin arzikin mu zai dawo duk da cewa mazajenmu da aka kashe ba zasu sake dawowa ba. Na fito daga yankin Batsari, kuma banji tsoron biyo hanyar da aka ce za'a biyo ba saboda imani da nayi akan cewa, jam'iyar PDP tana bisa kyakkyawar niya.
To amma ina batun zargin da ake yi cewar, jam'iyar ta PDP ita ce ta kawo wannan matsalar rashin tsaron tare da facaka da dukiyar al'umma? Masu bayar da amsar wannan tambayar dukkan su sun amsa tambayar ta hanyar yin tambaya. "Tsawon shekaru bakwai PDP ce ke mulki? Amma me ya canza? In baya ga ƙara shiga cikin matsalolin da kashi 100 cikin 100 me muka gani? Dubi yadda garin na Funtua yake a yanzu? Malam! Bari wannan maganar kawai.
A batun taron kuwa, zaiyi wuya ace ga adadin mutanen da suka halarce shi domin har waÉ—anda ba'ayi zato ba sun shi. Wannan mutumin mai suna Ashiru daga yankin Sabuwa, yace, "da nayi fushi da harkokin siyasa amma zowar wannan yaro ya sanya ni sake dawowa cikinta. Kuma jam'iyar PDP wadda can baya bani son a ambata mani ita, amma yanzu na gane cewar ita ce jam'iyar talakawa kuma mai son talakawa. Ba sai nace ga jam'iyar da nayi can baya ba. Kuma kaga wannan yaron, nace da zarar mun koma gida ya shaida mutane na cewar, daga yau mun shiga PDP kuma duk wani É—antakarar ta shi zamu zaba. Kuma ina tabbatar maka da cewa, duk yankin da nike fadi su ji zan gaya masu haka". To shin canjin sheka ne kayi? (cikin dariya) Ai in ana canza gari, to daga yau mun canza.
Saidai a kamar yadda ake cewa, ba'a ɓarin gari a kwashe lafiya, to a wannan taro anso ayi haka, domin an samu wasu tsagera sun nemi tayar da hankali, amma ba tare da ɓata lokaci ba jami'an tsaro suka ɗauki mataki akai. Har zuwa rubuta wannan rahoto, babu wani abu na tashin hankali ko ɓacewar wani abu da muka samu. To shin wannan taron ya nuna cewar, alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba kenan? Sannan taron zai kawo ƙarshen matsalar cikin gidan jam'iyar kamar yadda wasu ke cewa, inma har akwai matsalar?