SHIYYAR KUDANCIN KATSINA APC ZATA YI ZAGAYEN ƘARSHE A SATIN GOBE

SHIYYAR KUDANCI KATSINA APC ZATA YI ZAGAYEN ƘARSHE A SATIN GOBE 

Daga Jamilu Hashim Gora 

 A ranar Litinin, 15 ga watan Janairu na shekarar 2023 ne Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam’iyar APC Dr Dikko Umaru Radda tare datawwagar yakin neman zabensa zasu cigaba da gangamin yakin neman zabe.  wannan karon jirgin yakin neman zaben zai saukane a shiyyar Katsina ta Kudu da akafi sani da Shiyyar Funtua ko Karadua. 
 
Wakilinmu ya ruwaito cewa idan za’a iya tinawa, Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina a Karkashin Jam’iyar APC Dr Dikko Umaru Radda ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a ranar 31 ga watan October kafin kuma a kaddadamar da gangamin yakin neman zaben wanda ya wakana a ranar 5 ga watan December a karamar hukumar Faskari.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari da Shugaban Jamiyar APC na Jiha Alhaji sani Jb Daura da yan Majalisar Dokoki dana zartaswa da yan kwamitin yakin neman zabe karkashin jagorancin Arc Ahmed Dangiwa da magoya baya da yan uwa da abokan arziki suka halarci bikin kaddamar da gangamin yakin neman zaben. 
Bayan kaddamar da gangamin yakin neman zaben a karamar hukumar Faskari dake a kudancin jihar Katsina a ranar 5 ga watan December, jirgin yakin neman zaben ya kuma shilla zuwa Arewacin Jihar inda ya sauka a karamar hukumar Baure a ranar 7 December don cigaba da yakin neman zaben.
Dan takarar Gwamnan tare da kwamitin yakin neman zaben a karkashin jagorancin Arc Ahmed Dangiwa ya cigaba da kutsawa lungu da sako na mazabun dake fadin kananan hukumomin yankin don kai ziyarar bangirma da neman goyan baya da kuma ganawa da masu ruwa da tsaki da shuwagabannin al’umma da masu rike da sarautu inda ya zagaya mazabu 128 na kananan hukumomi 12 dake a shiyyar Daura da kuma mazabu 113 dake a kananan hukumomi 11 na shiyyar Katsina ta tsakkiya wanda ya kawo jimlar mazabu 241 na kananan hukumomi 23 da dan takarar gwamnan ya ziyarta.
Babban abinda ke da jan hankali a wancen lokacin shine, yadda dan takarar gwamnan Dr Dikko Radda ya shige gaba kuma ya jagoranci tawwagar yakin neman zaben ba tare da nuna tsoro ko gajiyawa ba a yankunan dake fama da matsanancin rashin tsaro a kananan hukumomin Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Dutsinma da kuma Kurfi inda wasu yan jamiyun adawa suke tinanin bai iya kutsawa.
Dr Dikko Radda ya shiga lunguna masu hatsarin gaske irinsu Zakka, Babban Duhu, Tsaskiya, Kuka Samu, Wagini, Danmusa, Yantumaki da sauran sassan kananan hukumomin Jibia da Kurfi da Dutsinma inda wasu yan bindigar sukai ikirarin bazasu bari a gudanar da gangamin yakin neman zaben amma duk da hakan da taimakon Allah da jajircewar Dan Takarar Gwamnan Dr Radda da kuma kyakkyawan tsari da kokarin kwamitin tsaro na gangamin yakin neman zaben, an shiga yankunan, kuma an fito lafiya ba tare da kashe ko kama koda dan tsako ba.
A dukkan wuraren da aka ziyarta, dan takarar gwamnan yayi alkauruka da dama ga al’umma mabanbanta, wanda zai cika idan Allah ya bashi damar zama gwamnan, a inda har yama fara cika wasu daga cikin alkaurukan daya dauka a garin Kwatta dake Karamar hukumar Mani wadanda suka bukaceshi daya gina masu rijiyar Burtsatsai don samun ingantaccen ruwan sha idan Allah ya bashi damar zama gwamnan, wanda anan take ya bada umarni a gina fanfan tuka tuka wanda yanzu haka har sun fara amfana dashi.
Dr Dikko Radda yayi alkurin yin duk mai yiwuwa don kare rayuka da dukiyoyin al’umma da bunkasa aikin gona da inganta ilimi da samar da ayyukanyi da inganta aikin gwamnati wanda yace sune a sawun gaba daga cikin kudurorinsa da ayyukan alherin da zai yi idan Allah ya bashi damar zama gwamnan jihar Katsina.
A dukkan wuraren da dan takarar gwamnan da tawwagar sa suka ziyarta, sun samu tarba daga dubban magoya baya da sukai tururuwa don tarbarsu a wani lokaci ma cikin duhun dare ana kade kade da wake wake na nuna shauki wanda hakan ya rinka sanya farin ciki da jindadi ga zuciyar dan takarar gwamnan wanda a wani lokaci guda ya zubda hawaye na farin ciki ganin yadda manya da yara, maza da mata sukai tururuwa a mahaifarsa ta Radda don tarbarsa a cikin dare.
Dan Takarar Gwamnan na jihar Katsina a karkashin Jam’iyar APC Dr Dikko Radda a lokacin da yake gangamin yakin neman zaben a shiyyoyin Katsina ta tsakiya da ta Arewa, ya samu kyaututtuka da dama da suka hada da Dawakai da Rakumi da Shanu da sauran Dabbobi da Al’qur’ani Mai Tsarki da Takobi da dai sauransu.
Daga cikin bayanan da aka gudanar a yayin da ake jawabi daga bakuna mabanbanta da suka hada da shugaban jam’iyar APC na jiha Alhaji Sani Jb Daura da shugaban kwamitin yakin neman zabe Arc Ahmed Dangiwa da sauran yan takarkari, anyi kira da a zabi yan takarar jam’iyar APC tin daga kasa har sama, aka kumayi tawassali da ayyukan cigaba da jam’iya mai mulki ta APC a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta samar a matakin jiha a bangaren ilimi da suka hada da gina sabbin makarantu tare da gyara wadanda suka lalace, samar da kayan koyo da koyarwa tare da daukar sabbin malamai da kuma horas da tsaffin, a bangaren kiwon lafiya, an gyara manyan asibitocin garin Katsina da Daura da Funtua tare da daga darajar wasu da samar da kayan aiki da ma’aikata. A bangaren manyan ayyuka kuwa, akwai gadar kasa da sama da aka gina a kofar kaura da kofar kwaya da tsohon gidan gwamnati daSsamar da ruwan sha, da tallafawa mata da matasa.
A bangaren gwamnatin tarayya kuwa, akwai shirin rage radadin talauci da ake kira conditional cash transfer a turance inda ake baiwa masu karamin karfi kudade kai tsaye acikin asusun ajiyarsu nabanki da shirin ciyar da yara yan makarantun firamare abinci da shirin N-Power da shirin bunkasa kanana da matsakaitan sana’oi da sauransu.
Tabbas ko shakka babu, zabar dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin Jamiyar APC Dr Dikko Umaru Radda dama sauran yan takarar jamiyar APC a zabuka masu zuwa zai baiwa jihar Katsina dama Nigeria baki daya damar cigaba da samun tagomashi da ayyukan cigaban al’umma a fannoni daban daban.
Don hakane ma ake bukatar yan jihar Katsina dama Nigeria baki daya wadanda suka isa shekarun kada kuri’a kuma suka yanki katin zabe dasu tabbatar da sun amshi katin zaben su tare da adanshi don zabar shuwagabannin da suke da zummar kawo masu cigaba a zabukan kasa dake tafe.

1 Comments

Previous Post Next Post